1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lafiya Uwar Jiki- Kowa ya kwana Lafiya shi ya so

January 22, 2009
https://p.dw.com/p/DrGM
Hoto: CORBIS

Lafiya Uwar Jiki- Kowa ya kwana lafiya shi ya so.

Shirin Ji Ka Ƙaru anan yana so ya nuna yadda rayuwa take da sauƙi in an bi umarni. Ganin yadda cuttuttuka iri-iri suka addabi Afirka. Yanzu an samu sa’ida saboda shirin ji ka karu ya kawo sauƙi ta hanyar saurarommu a rediyo, ba sai ka je neman litattafai ba.

Sanin kowane cewa cutar zazzabin cizon sauro da aka fi sani da malariya, ta fi ɗaukar rai a Afirka. A ƙalla jariri ɗaya ke rasuwa a duk daƙiƙa talatin a Afirka a sanadiyar zazzabin na cizon sauro. Ba cutar zazzabin kadai ke sanadiyyar asarar rayuka ba, har ma da shan gurɓataccen ruwa wanda ke sa cutar zazzaɓin typhoid, akwai kuma cutar mummunar ƙiba wadda ta fara zama ruwan dare a Afirka.

Saboda haka rigakafi ya fi magani, idan aka bi shawarar masana ilimin kimiyya, to za a zauna cikin ƙoshin lafiya, a wani shirin wasan kwaikwayo a rediyo, Ji Ka Ƙaru zai bi wasu yara biyar dan ganin yadda za su tafiyar da rayuwarsu bayan sun bar gidajensu na haihuwa. Mu ga ko za su bi shawarar kiwon lafiya.

An yi shirin na Ji ka ƙaru a harsuna shidda, waɗanda suka haɗa da Ingilishi, Kiswahili, Faransanci, Hausa, Portuguese, da Amharic.

Shirin Ji Ka Ƙaru na samun gudunmuwa ne daga ofishin hulɗa da ƙasashen waje na ƙasar Jamus.