1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyawun alkawari cikawa inji Tony Blair

April 25, 2007
https://p.dw.com/p/BuMu

P/M Britaniya Tony Blair ya yi kira ga manyan kasashe masu arziki su cika alkawuran da suka yi na taimakawa raya kasashen Afrika. Blair wanda ya gana da tsohon sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan da shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin domin tattauna cigaban da aka samu na aikin da aka dorawa kwamitin lura da cigaban kasashen na Afrika. An kafa kwamitin ne a watan Yunin da ya gabata karkashin jagorancin tsohon sakataren majalisar dinkin duniyar Kofi Annan. Tony Blair yace kasashe masu arziki na yammacin turai za su kuka da kan su idan suka ki cika alkawuran da suka yi na tallafawa nahiyar ta Afrika. Idan baá manta ba shekaru biyu da suka gabata a taron G8 ta kasashe masu cigaban masanaátu a Gleneagles wadda Britaniya ta jagoranta, manyan kasashen suka yi alkawarin yafe bashin da suke bin kasashen Afrika da kuma rubanya taimakon da suke bayarwa ya zuwa shekara ta 2010. A nata bangaren shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi alkawarin cewa Batun nahiyar Afrika zai kasance a kann gaba a jadawalin taron da zaá gudanar a bana na kungiyar ta G8 da Jamus zata karbi bakuncin sa.