Kyawawan manufofin Köhler game da Afirka | Siyasa | DW | 01.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kyawawan manufofin Köhler game da Afirka

ƙasashen Afirka na ci gaba da tuna kyakkyawar hulɗar da ta wakana tsakaninsu da Horst Köhler a tsahon shugabancin Jamus da yayi na shekaru shida.

default

Köhler tsakanin yaran Rwanda

Tun a jawabinsa na farko bayan ɗarewarsa kan kujerar shugabancin Jamus shekaru shidan da suka gabata ne, Köhler ya fito fili ya bayyana wa majaisar dokokin ƙasarsa cewa zai bai Afirka fifiko a wa'adin mulkinsa. Saboda hakane a duk lokacin da yayi rangadi i zuwa wata ƙasa , sai Horst Köhler yayi amfani da wannan dama wajen taɓo batutuwan da ke ci ma ƙasashen na Afirka tuwo a ƙwarya.

"ya ce a ƙasashen Afirka an kafa ƙungiyoyin taimakon kai da kai. Mutane na bukatan waɗannan ƙungoyoyi wajen inganta halin rayuwarsu. Manoma ga misali na karo karo wajen sayan taki da za su amfani da shi a gonakinsu, tare da haka rijiyoyi. ƙungiyoyi na Afirka har ila yau na tashi tsaye domin yaƙi da cin hanci, tare da sa aido kan yadda gwamantoci ke gudanar da ayyuikan raya ƙasa. Mata kuma na hoɓɓasa a inda suke haɗa kai domin gina makarantu da kuma cibiyoyin yaƙi da cutar AIDS"

Horst Köhler in Afrika Treffen mit Mandela in Mosambik

Horst Köhler da Nelson Mandela

Sai dai matakin tsuke bakin aljuhu da ya sa gwamanatocin Afirka ɗauka a lokacin da ya riƙe mukamin shugaban hukumar lamini ta duniya, ya sa ƙasashen na Afirka ɗari-ɗari rungumar shi köhler hannu biy-biyu. Ko da shi ke ya samu karɓuwa daga bisani. A cewar Ulf Engel , masani a kan nahiyar Afirka na jami'ar Leipzig.

"Ya ce a Afirka da akwai mutanen da suka fara shafa wa Köhler kashin kaji bayan aiwatar da manufofin hukumar lamini da yayi a wannan nahiya. Sai dai bayan hawansa kan gadon mulkin jamus, ya ƙaddamar da sabon babin danganta da ya sa shi samun kwarjini a tsakanin 'yayan wannan nahiya. Dangantaka ta ƙuta da ƙut da ya gudanar da waɗannan ƙasashe ne ya wanke shi daga zargin da aka yi masa a baya."

Tsarin da shugaban mai murabus ya girka mai taken "dangantaka da Afirka" ya bayar da damar ƙarfafa hulɗa kai tsaye tsakanin Jamus da takwarorinta masu tasowa na Afirka. Hakazalika Horst Köhler ya samar ma ƙasashen Afirka kafar inganta dangantarsu da ƙasashen yammacin duniya a fannoni da suka haɗa da na ciniki. Ba a kuma bar Köhler a baya ba wajen bai wa matasan Jamus da kuma na Afirka damar ƙulla danƙon zumunci a fannoni al'adu da kuma zamantakewa tsakaninsu ba. Ulf Engel na jami'ar Leipzig yayi tsokaci.

Horst Köhler in Afrika Mosambik

Köller da shugaban Mozambik

"ya ce duk abubuwan da yayi ma aAfirka waɗanda ake gani a ƙasa ne. Yayi ta fitowa ƙarara ya na baiyana alƙiblar da ya kamata ƙasashen yammacin duniya sun fiskanta domin bai wa Afirka damar bunƙasa. To amma inda gizo ke saƙa a shekaru shidan da ya shafe na shugabanci,shi ne ƙin sauraran koke koken nasa game da afirka da fadar mulki ta Berlin ba ta yi ba."

Babu tabbas game da ko shugaban da zai maye gurbin Horst Köhler zai bai ma Afirka fifiko, koko a' a. A saboda haka ne ake ganin cewa murabus na Köhler ya zama wata dama da gwamanti za ta samu na rage tallafin raya ƙasa da ta ke ware ma kasashen Afirka a wannan marra na matsin tattalin arziƙi. 

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu