1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyautar Yabo ta Sacharow ga Majalisar Dinkin Duniya

Mohammad Nasiru AwalJanuary 29, 2004
https://p.dw.com/p/BvmE


Yayin da ya ke karbar wannan kyautar a madadin dukkan ma´aikatan MDD, sakatare janar na MDD Kofi Annan ya ba kowa mamaki, inda yayi amfani da wannan damar wajen sukar lamirin kungiyar tarayyar Turai EU dangane da manufofinta da suka shafi zaman baki da kuma ´yan gudun hijira a cikin kasashen kungiyar. Zauren majalisar ta Turai dai ya cika da jama´a a lokacin da ake bikin ba da wannan lambar yabo ta Andrey Sacharow. Ko shakka babu nan da ´yan shekaru kalilan masu zuwa nahiyar Turai zata kasance mai cike da tsofaffi, saboda haka wannan nahiya na bukatar baki masu takardun izinin zama cikin kasa, don samun wani sahihin tsari na tattalin arziki da zaman jama´a, inji Annan sannan ya kara da cewa:

Annan:
"A bayyana ya ke cewar baki ´yan ci-rani na bukatar Turai, haka ita ma Turan tana bukatar wadannan baki. Duk wata Turai da ta rufe kofofinta to zata kasance matalauciya, raunanniya kuma tsohuwa. Amma Turan da ta bude kofofinta zata zama mai adalci, wadatacciya, mai kwari kuma matashiya, amma bisa sharadin cewa zata samar da wata sahihiyar doka da ta shafi baki ´yan ci-rani."

Annan ya yi tuni da cewa a cikin karnin da ya gabata, miliyoyin Turawa sun yi kaura daga kasashensu na asali bisa dalilan da suka sanya yanzu mutane ke yin kaura daga kasashe masu tasowa. Bai kamata a dauki baki a matsayin ma´aikata kawai ba, a´a kamata ya yi a shigar da su cikin harkokin yau da kullum na jama´a, inji Annan, inda ya kara da cewa:

Annan:
"Ana bukatar yin gyara ga tsarin ba da mafakar siyasa a Turai domin hanzarta duba takardun masu neman mafaka tare da ba da kariya da kuma magance matsalolin ´yan gudun hijira. Ya zama wajibi kasashen nahiyar Turai su samar da wani kwakkwaran tsarin ba da mafaka na bai daya tsakaninsu."

Shi kuwa a nasa bangaren shugaban majalisar shawara ta tarayyar Turai a yanzu kuma ministan harkokin wajen Jamhuriyar Ireland, Brian Cowen ya fadawa wani taron manema labarai cewa Turai na kokarin daidaita manufofinta na mafakar siyasa da kuma na baki ´yan ci-rani.

Cowen:
"Na san cewa mu ne kasa ta 6 ko 7 a fadar shugabancin kungiyar EU da muka yi kokarin cimma wata madafa game da ka´i´dojin da muka shimfida a cikin watan oktoban shekarar 1999. Mun kuduri aniyar fadada fannonin ´yancin walwala, tsaro da kuma adalci a cikin kungiyar tarayyar Turai."

Ita kuwa tarayyar Jamus so take a tsananta dokokin ba da mafakar siyasa a kungiyar EU, to sai dai har yanzu ba´a cimma wani tudun dafawa game da wata doka ta bai daya ga kungiyar ba. Masu ra´ayin mazan jiyya a cikin majalisar Turan na ganin cewa dole ne a kyautata halin rayuwa a cikin kasashen da jama´arsu ke yin kaura zuwa ketare ta yadda ba zasu ji kwadayin fita waje ba.

A cikin jawabin da yayi, sakatare janar na MDD Kofi Annan ya jawo hankalin jama´a kan cewar mutum 7 daga cikin ´yan gudun hijira 10 ke samun mafaka a cikin kasashe masu tasowa.

Shi kuwa a nasa bangaren shugaban majalisar dokokin kungiyar EU Pat Cox yabawa yayi da ayyukan ma´aikatan MDD wajen shimfida demukiradiyya da kare hakkin dan Adam. Inda ya ce suna sadaukar da rayukansu, sannan ya ba da misali da mutane 22 da suka mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai kan hedkwatar Majalisar dake birnin Bagadaza a ran 19 ga watan agustan bara. Pat Cox ya yayi bakin ciki game da cewar da yawa daga cikin wadanda suka samu kyautar yabon a bara ba su halarci gun bikin na bana ba, saboda an tsare su a kasashensu kamar alal misali Leyla Zana, wadda ke tsare yanzu a gidan kurkukun kasar Turkiya bisa zargin taimakawa kungiyar Kuradawa ta PKK.

Daga cikin mutanen da suka halarci gun bikin ba da kyautar yabon da aka lakabawa sunan Andrey Sacharow rikakken mai adawa da gwamnatin tsohuwar Tarayyar Sobiet, akwai uwargidar tsohon wakilin MDD na musamman a Iraqi Sergio Vieira de Mello, wanda shi ma ya rasa ransa a wannan hari.