1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyamar Manufofin Amurka A Kasashen Larabawa

October 27, 2004

Martabar Amurka ta zube kwata-kwata a kasashen Musulmi da na Larabawa sakamakon manufofinta a Iraki da goyan bayan da take wa Isra'ila a yankunan Larabawan dake karkashin mamayenta

https://p.dw.com/p/Bvf6

A halin da ake cikin yanzun dai babu wata kasa ta Musulmi ko ta Larabawa, inda limamai ba sa sukan lamirin manufofin Amurka a hudubarsu ta sallar juma’a. Limamai kan yi suka da kakkausan harshe akan manufofin Isra’ila a yankunan Larabawa dake karkashin mamayenta da manufofin Amurka a Iraki da kuma matakan kasa da kasa na yaki da ta’addanci, wanda a ganinsu ba kome ba ne illa wata manufa ta yaki da Musulunci da kuma kyamar al’adun Larabawa. Amma fa wadannan Limaman ba manufarsu ce su rura wutar rikici ba, hali ne da ake ciki a dukkan kasashen Musulmi na duniya, inda babu wani dake kaunar Amurka ko Isra’ila, in banda a rika yi musu tofin Allah tsine. Dukkan Larabawan da aka tambayi albarkacin bakinsu bayan sallar juma’a a masallacin Azhar mai dadadden tarihi sun zargi Amurka da adawa da Larabawa, inda a baya ga muzantawar da sojojinta ke wa al’umar Iraki dake kuma ba da cikakken goyan baya ga Isra’ila a matakan da take dauka akan Palasdinawa. Wani Balaraben da aka tambayi albarkacin bakinsa cewa yayi:

Allah Waddan Bush, Allah Waddan Sharon, Allah Waddan Amurka, wacce ba ta da adalci. Wajibi ne a mayarwa da Palasdinawa kasarsu a kuma ba wa Irakawa damar daukar kaddararsu a hannunsu. Allah Waddan Bush da ‚yan kanzaginsa P/M Birtaniya da Sharon.

Wata Balarabiyar bayyana mamakinta tayi dangane da yadda ake kwatanta masu fafutukar neman kwaco kasarsu tamkar ‚yan ta’adda. Idan har Bush ya ce masu neman hakkinsu ‚yan ta’adda ne, to shi kuma mene ne matsayinsa. Ai ya fi ‚yan ta’addan ma barna. Akwai alamomin dake nuna cewar al’amura zasu dada yin tsamari a zirin Gaza da kasar Iraki. A can kasar Masar dai ba wanda ke zaton samun wani kyakkyawan sauyi, musamman ma idan har George Bush ya sake darewa kan kujerar mulkin Amurka. Bisa ga ra’ayin Muhammed Sa’id daga cibiyar nazarin manufofin siyasa ta Al-Ahram dake birnin Alkahira, mai yiwuwa a samu wata ‚yar sararawa idan Kerry ya cimma nasara, saboda ga alamu zai janye sojan Amurka daga kasar Iraki kuma gwamnatinsa zata yi taka-tsantsan a manufofinta dangane da Bagadaza: Duk wanda yayi bitar manufofin shugaba Bush dai zai ga matakai na rashin imani take dauka, ba sani ba sabo, a dukkan manufofinta na ketare. Ba abin da ya taba ci mata tuwo a kwarya a game da mawuyacin halin da al’umar iraki ke ciki. Wannan manufar ta sake farfado da akidar kyama da kiyayya da ta addabi nahiyar Turai a cikin shekarun 1930.