1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ethiopia ta ƙudiri aniyar cimma shirin ƙarni na MDG

August 14, 2010

Ethiopia ta ƙudiri aniyar cimma shirin ƙarni na Majalisar Ɗinkin Duniya, MDG

https://p.dw.com/p/Ons2
Mata masu juna biyu a wani asibiti a ƙasar Ethiopia .Hoto: Sarah Bomkapre-Kamara

Yawancin mata a ƙasar Ethiopia waɗanda basu wuce shekarun haihuwa ba kan rasa rayukansu walau dai a lokacin da suke da juna biyu ko kuma a lokacin haihuwa. Hasali ma dai yawan matan da kan rasa rayukansu a yayin haihuwa sun fi adadin da kan rasu a sakamakon cutar Malaria da HIV/AIDS da kuma tarin fuka idan aka haɗa su baki ɗaya. 

A yanzu haka dai ƙasar Ethiopia ita ce kan gaba wajen mace macen mata masu juna biyu a Afrika. A kowace shekara akan samu mata 670 da ke mutuwa daga cikin adadin mata masu ciki kimanin 100,000. Ƙididdiga ya nuna mata shida ne kacal daga cikin ɗari ke iya samun taimakon ƙwararrun ma'aikatan jinya a lokacin da suke da juna biyu ko kuma a lokacin haihuwa. Hakan na faruwa ne kuwa saboda ƙarancin ma'aikatan jinyar inda akan sami ungozoma ɗaya da likitoci biyu rak ga marasa lafiya 100,000

Domin sauya wannan fasali da kuma inganta harkar kiwon lafiya a ƙasar gwamnatin Ethiopia da Majalisar Ɗinkin Duniya suka ƙaddamar da yunƙurin cimma shirin sabon ƙarni na Millenium Development Goal nan da shekara ta 2015 domin rage da kimanin rabi adadin mace macen mata masu juna biyu a lokacin haihuwa. Gangamin na ƙasa baki ɗaya ya ƙudiri cewa ba za'a yi sake wata mace ta rasa rayuwarta wajen haihuwa ba. Shirin ya sami goyon bayan ƙungiyoyin addini da suka haɗa da na musulmi da Kirista inda suke faɗakar da matan fa'idar tsarin iyali.

Asiya Mohammed uwar gida ce mai shekaru 30 wace kuma ke da yaya takwas. Tana zaune ne a wani ƙaramin kauye da ake kira Aseliso mai tazarar kilomita 500 daga Addis Ababa babban birnin ƙasar Ethiopia kuma kusa da kan iyaka da Somalia. A wannan ƙauye babu kayayyakin zamani na more rayuwa da harkokin sufuri dana lafiya.

" A da bana amfani da dabarun tsarin iyali a saboda haka kusan duk shekara sai na haihu. A wancan lokaci bamu da cibiyar sha magani, abin dai ya kasance yanayi mawuyaci a garemu. Iyaye da dama da yara ƙanana sun rasa rayukansu a sanadiyar cutukan Malaria, Amai da gudawa da sauran cutattuka".

MDG Tadschikistan Müttersterblichkeit
Yunƙurin likitoci domin ceto rayuwar mata masu juna biyu.Hoto: DW

Sai dai kuma Asiya da sauran mata a ƙauyen na Seliso sun yi sa'ar samun Sheik Salim Woda. Malamin mai shekaru 50 a duniya shine shugaban al'umar musulmi a ƙauyen. Sheik Salim na baiwa matan shawarwari kan al'amuran da suka shafi rayuwa da tsarin iyali da kuma yadda za su yi haƙuri da juna bugu da ƙari da sanar da su matakan da za su ɗauka domin rage mace macen mata da ƙananan yara.

" Alkur'ani mai tsari ya baiwa mata damar ɗaukar matakan tsara tazarar haihuwa, alal misali shekaru biyu a tsakanin haihuwa. Kakanninmu sun ɗauki irin waɗannan matakai na gargajiya a da, amma a yanzu sauƙi ne ya samu ta yi amfani da kwaroron roba. Saboda haka haƙƙi ne da ya rataya a wuya na in sanar da matan karkara cewa a addinance ba laifi bane ka yi amfani da irin waɗannan dabarun tsara tazarar haihuwa kuma na lura suna fahimtar hakan. A yanzu a wannan ƙauyen namu, ana samun ƙoshin lafiyar iyaye mata da jariransu".

A yanzu haka dai ƙaramar hukumar ta gina ɗan ƙaramin Asibiti a wannan  ƙauye domin kula da lafiyar mata masu ciki da kuma jarirai. Wannan dai wani matakin cigaba ne muhimmi aka samu a wannan gari.

Yanzu dai ƙasar Ethiopia na da sauran shekaru biyar domin cimma wa'adin ƙarni na Majalisar Ɗinkin Duniya wato Millenium Development Goal domin rage mace macen mata da ƙananan yara da kimanin rabi. Wanna babban ƙalubale ne musamman a ƙasar dake zama ɗaya daga cikin mafi talaucin ƙasashe a duniya. Sai daraktan kiwon lafiya na Dire Dawa Tsigereda Kifle yace suna da imanin za su iya cimma wannan wa'adi.

Mawallafa : Yohannes Gebreegziabher / Abdullahi Tanko Bala

Edita : Umaru Aliyu