1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyakkyawan shugabanci zai ceto Najeriya

April 2, 2010

Shirya zaɓe na gaskiya da adalci da kyakkyawan shugabanci zai taimaka wajen magance matsalolin Najeriya

https://p.dw.com/p/MmFb
Muƙaddashin shugaban Najeriya Dr. Goodluck JonathanHoto: AP

A yau za mu fara ne da tarayyar Najeriya. A wani rahoto da ta buga jaridar Handelsblatt ta fara ne da tambayar: Shin Najeriya na kan durƙushewa? Jaridar ta rawaito masu lura da al'amuran yau da kullum na cewa Najeriya wadda ta fi kowace ƙasar Afirka arzikin man fetir ka iya faɗawa ciki wani yanayi na rushewa. Ta ce watannin da dama na giɓi a madafun iko, rikice rikicen addini da rigingimu a yankin Niger Delta mai arzikin man fetir sun jefa Najeriya mai yawan al'umma fiye da miliyan 140 cikin wani hali mai haɗari na rashin tabbas. Shirya zaɓe na adalci a shekara mai zuwa da aiwatar da kyakkyawan tsarin siyasa gwamnati za ta iya shawo kan matsalolin ƙasar kamar cin hanci da rashawa da rashin hasken wutar lantarki da dai sauransu.

Omar Hassan Ahmad al-Bashir Präsident Sudan
Shugaban Sudan Hassan al-BashirHoto: picture-alliance/ dpa

Shirye shiryen gudanar da zaɓe a ƙasar Sudan na fuskantar koma baya sakamakon janyewa daga zaɓen daga 'yan takarar neman shugabancin ƙasar na ɓangaren jam'iyun adawa. Da waɗannan kalaman jaridar Tageszeitung ta fara rahoton game da zaɓen na Sudan. Ta ce kwanaki ƙalilan gabanin a gudanar da zaɓen dake zama irinsa na farko cikin shekaru 24 da ya ƙunshi jam'iyu barkatai a Sudan, babu tabbas ko za a gudanar da zaɓen a ranar 11 ga watannan na Afrilu. 'Yan adawar musamman na kudancin ƙasar dai na fargabar cewa za a tabƙa babban maguɗi a zaɓen, domin shugaba Al-Bashir ya bari an buga katunan zaɓe a cikin harshen Larabci kaɗai maimakon na turanci harshen da ake amfani da shi a kudancin ƙasar.

Strassenszene in Nairobi Kenia Verkehr
Hada-hada a birnin NairobiHoto: picture-alliance/dpa

Alƙalan ƙetare ga Kenya, inji jaridar Süddeutsche Zeitung tana mai nuni da ƙasar Kenya a matsayin wata ƙasar Afirka da a tarihin baya bayan nan ta sha yabo saboda kwanciyar hankali da lumana da suka wanzu a cikinta. 'Yan yawon shaƙatawa daga Turai da Amirka sun yi kwarara wannan ƙasa cikin kwanciyar hankali. To sai dai abubuwa sun ɗauki sabon salo sakamakon maguɗin da aka tabƙa a zaɓen shekarar 2007, wanda ya haddasa mummunan tashin hankali da kashe kashen juna tsakanin ƙabilun ƙasar. Abin da ya fi muni shi ne har yanzu ba a hukunta masu hannu a rigingimun ba, saboda gazawar shugabannin Kenya na gurfanar da su gaban kotu, domin daga cikinsu akwai masu samun ɗaurin gindin hukumomin ƙasar. Amma yanzu kotun ƙasa da ƙasa ce za ta yi shari´ar. Kuma idan mahukuntan Kenya ba su ba da haɗin kai ba dole ne ƙasashen yamma za su ɗauki matakan jan kunnenta.

Bari mu kammala da jaridar Tageszeitung wadda ta yaba da kwaskwarima da aka yiwa harkar cinikin ma´adanan ƙarƙashin ƙasa a gabashin Kongo kwaskwarima. Tun ba yau ba gamaiyar ƙasa da ƙasa ke suka cewa madugan yaƙi a wannan yanki na amfani da kuɗin cinikin suna sayen makaman da suke yaƙi da su. Jaridar ta ce matakan magance wannan rikici a cikin gida shi ne mafi dacewa, to amma ana buƙatar taimako daga gamaiyar ƙasashen duniya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala