Kwas don sajewar iyaye baki a Jamus | Zamantakewa | DW | 30.07.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Kwas don sajewar iyaye baki a Jamus

A ƙoƙarin da hukumomi da sauran ƙungiyoyimasu zaman kansu ke yi na ƙara shigar da baƙi ´yan ƙaƙagida a rayuwar yau da kullum a nan Jamus, an fara wasu ƙwasa ƙwasai ga iyayen yara.

default

Kwas don sajewar baƙi a Jamus

A waɗannan kwasa-kwasan baƙin na koyan harshen Jamusanci tare da ƙara musu sani game da ilimin da ake bawa ´ya´yansu a makarantun ƙasar.

A ranar 8 ga watan Yuli ministah harkokin cikin gidan Jamus Wolfgang schäuble a birnin Berliny a ƙaddamar da wata yekuwa mai taken koyan Jamusanci da sanin ƙasar Jamus. Manufar wannan shirin ita ce ƙarfafa guiwar iyaye maza da mata da suka yi ƙaura zuwa tarayyar Jamus shiga cikin kwasa-kwasai na ba da ilimin sajewa da ´yan ƙasa. A waɗannan ƙwasa-kwasai ba harshen Jamusanci kaɗai ake koyarwa ba, ana kuma ilmantar da iyayen kan yadda ake tafiyar da makarantun nasare, firamare da sakandare da kuma cibiyoyin koyan sana´o´i a nan Jamus. A ƙarshe ana fata iyaye za su iya bawa ´ya´yansu taimakon da suke buƙata da ya shafi makarantarsu.

Kopftuch auf dem Kirchentag - BdT

Ɗaya daga cikin makarantun da ta fara wannan aiki ita ce makarantar sakandare dake unguwar Kreuzberg a birnin Berlin. Kimanin shekaru uku da suka gabata makarantar tare da ƙungiyar iyaye Turkawa mazauna yankin Berlin da Brandenburg suka cimma yarjejeniyar haɗin kai don tafiyar da wannan aiki. Tun daga wannan lokaci a kullum da safe iyaye da malamai ke haɗuwa a wani ɗakin karatu na wannan makaranta. Iyaye mata tsakanin 10 zuwa 15 ɗaukacinsu sanye da ɗan kwalli ke halartar wannan kwas ɗin a kullum ranar Allah Ta´ala.

Ga dai ra´ayoyin wasu daga cikin iyayen, musamman waɗanda ke jin harshen Jamusanci.

Kopftuch.jpg

“A shirye na ke a kullum in san abin da ke awaki a makarantar da ɗa na yake zuwa da kuma dukkan abubuwan dake faruwa. Fata na shi ne in samarwa ɗa na abu mafi kyau.”

“Muna tattaunawa game da ´ya´yan mu da abubuwan da ke wakana a nan. Muna tattaunawa game da abubuwan da suke yi a makaranta ko mai kyau ko maras kyau.”

“Haƙiƙa kam yana da kyau ka san wasu mutane daban kuma ka samu ƙarin ƙawaye. Taruwarmu a nan muna shan shayi, muna musayar ra´ayoyi game da makarantun ´ya´yan mu abu ne mai fa´ida.”

Ko shakka babu ba saboda shan shayi ko gahawa ya sa ake wannan haɗuwa ba inji Dorothea Illi daga ƙungiyar iyaye Turkawa. Ita dai Dorothea Illi ita ke ba da shawara akan batutuwan da suka shafi makaranta da renon yara kuma ita ke jagorantar wannan aiki, ta yi karin bayani tana mai cewa.

“Wannan wurin haɗuwa da muke kira wurin shan shayi ko gahawa na zaman wani dandali inda ake maraba da sauran al´adu a makaranta, domin bawa iyaye damar zuwa makarantar. Babban burin wannan aiki shi ne iyayen su kasance a cikin harkokin gudanarwar makaranta. Hakan kuwa wata babbar dama ce don sanin juna tsakanin iyaye da malamai, amma ba sai wata matsala ta kunno kai ba tukuna.”

A kullum Illi a shirye ta ke ta saurari duk mai son magana da ita musamman idan wata matsala ta kunno kai. Tana taimakawa wajen cike fom shiga tsakani don yin sulhu musamman akan sakamakon jarrabawar ´yan makaranta. Tana ƙoƙarin ganin an samu kusanta tsakanin iyaye mata da kuma makarantun Jamus dake zama baƙon abu ga ɗaukacin iyayen.

Kinder in Kreuzberg Kindergarten

“Da yawa daga cikin iyayen dake zuwa nan wurin wato akasari baƙin, hatta su kansu Jamusawan ma ba su da cikakkiyar masaniya game da abubuwan da ke wakana a makaranta saboda haka suke masa mummunar fahimta. Amma hakan ya fi tsauri a tsakanin baƙin waɗanda sau tari suke jin cewa ana nuna musu wariya kasancewarsu baƙi. Idan wata matsala ta taso sai su ce malami ne ba ya ƙyaunarsu domin su baƙi ne a cikin ƙasa.”

Dorothea Illi ta ci-gaba da cewa ilimi na da muhimmanci ƙwarai da gaske ga mata, amma a lokuta da dama ba sa iya taimakawa ´ya´yansu yadda ya kamata, musamman waɗanda suka manyanta domin ba su iya harshen Jamusanci sosai ba.

Daga cikin waɗanda suka halarci zaman iyaye a wannan karo har da wasu mata matasa su uku, biyu sanye da ɗan kwali suna zantawa da juna da harshen Jamusanci. A kowace safiya Nuran Ziath ita ce ta farko dake zuwa wannan wuri kuma ita ta ƙarshe da ke barin wurin. Nuran mai ´ya´ya uku tana ba da gagarumar gudunmawa a wajen haɗuwar iyayen kuma a sane tana nemawa ´yar ta makarantar firamare mafi daraja domin a lokacin da take yarinya ba ta samu wannan gata ba. Ga dai abin da take cewa.

“Mahaifiya ta ba ta iya harshen Jamusanci ko kaɗan ba. Ba ta taɓa halartar wani taron iyayen yara ba domin ba ta iya Jamusanci ba. Saboda haka tun ina ƙarama na ƙuduri aniyar tallafawa ´ya´ya na idan na girma, domin su samu sauƙin abubuwa. Saboda haka na ke musu Jamusanci kaɗai.”

Sau da yawa dai iyayen da ba su iya Jamusanci ba, ba su da ƙarfin halin faɗawa hukumomin makarantu ra´ayoyinsu, inji Nuran Ziath. Ta ce su na jin tsoro ka da a yi musu mummunar fahimta. Saboda haka wurin haɗuwa ke zama wani dandalin taimakon kai da kai. Matan da suka naƙalci harshen Jamusanci ƙwarai da gaske na taimakawa waɗanda ba su iya ba ko ta hanyar rubuta wasiƙa da dai sauransu, inji Nurn Ziath sannan sai ta ƙara da cewa.

“Wannan wurin ya fi ƙarfin wani wurin haɗuwa don shan shayi. Matan dake zuwa nan wurin na son kafa wata gamaiya ce. Mutane ne da suka duƙufa don taimakawa ´ya´yan su a harkokin na neman ilimi.

Mawallafa: Tina Heidborn/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin