Kwarya kwaryar yarjejeniyar sulhu akan Darfur | Labarai | DW | 26.04.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwarya kwaryar yarjejeniyar sulhu akan Darfur

Kungiyar gamayyar Afrika Au ,ta gabatar bangarori biyu dake adawa da juna a dangane da rikicin Darfur dake yammacin sudan,kwarya kwaryar yarjejeniyar sulhu ,inda tayi kira garesu dasu rattaba hannu kafin karshen wannan makon.Wannan shirin dai yazo ne adaidai lokacin da Komitin sulhun mdd ,ya kakabawa wasu manyan jamian sudan 4 ,takunkumin tafiye tafiye dana harkokin tattali,wadanda ake zargi da hannu a rikicin lardin darfur daya ki ci yaki cinyewa.Rahotanni dai na nuni dacewa,gaza cimma sulhu ayayin cikan waadin ranar 30 ga wannan wata,zai iya haifar da karin kakabawa wasu jamian sudan din takunkumi.

Daya gabatar da kwarya kwaryar yarjejeniyar wa bangarorin biyu a daren jiya a Abujan Nigeria,mai shiga tsakani na Au Salim Ahmed Salim,ya bukacesu dasuyi nazari sosai kann shirin kafin su amince da ita.Ya nanatawa bangarorin biyu cewa yanzu lokaci yayi da zasu cimma daidaito,domin idanun duniya na kansu,na ganin cewa an gano bakin zaren warware rikicin Darfur din daya kashe mutane sama da dubu 300.

 • Kwanan wata 26.04.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6m
 • Kwanan wata 26.04.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu6m