Kwarjinin shugaba Bush ya zube a idon Amurikawa. | Labarai | DW | 10.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwarjinin shugaba Bush ya zube a idon Amurikawa.

A ƙasar Pakistan,a na ci gaba da ɓarin wuta, tsakanin dakarun gwamnati da wasu yan takife, wanda su ka yi kaka gida, a masalacin Lal Masadjid da ke birnin Islamabad.

Da asubahin yau ne, sojojin gwamnati su ka yi wa wannan massalaci durra mikiya,an kasa shawo kan yan takifen ta hanyar tantanawa

Rahottani daga ƙasar sunce ya zuwa yanzu fiye da mutane 50 su ka rasa rayuka, wanda su ka haɗa da madugun yan takifen, AbdulRasheed Ghazi.

Kakakin rundunar gwamnati, Jannar Arshad,ya ce sun zaƙulo Mullah Ghazi, daga wata maɓuya, dake ƙarƙashin ƙasa, tare da wasu tsageru 5 masu tsaran lafiyar sa.

Jannar Arshad ya ci gaba da cewa, sun sami asara sojojin 8 a cikin wannan arangama, wadda a cewar sa, ba asan ranar ƙarewar ta ba, ta l´akari da turjewar da yan takifen ke ci gaba da yi.