Kwararru sunce Iran zata samu makaman nukiliya nan da shekara 5 | Labarai | DW | 03.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwararru sunce Iran zata samu makaman nukiliya nan da shekara 5

Wani rahoto da kwararru akan harkokin nukiliya na Rasha suke niyyar mikawa hukumar kula da harkokin waje da tsaro ta Rasha a gobe asabar,ya baiyana cewa,ya kamata kasashen duniya sun kwan da sanin cewa,kasar Iran zata samu kera makaman nukiliya nan da akalla shekaru 5.

Kanfanin dillacin labaru na Interfax ya ruwaito rahoton na cewa,wasu daga cikin kwararrun sunyi imanin cewa Iran zata samu wadannan makaman cikin watanni 6 zuwa shekaru 2,da dama daga cikinsu kuma sunce zuwa shekaru 5.

Wannan rahoto kuwa ya fito ne bayan Iran da Kungiyar TaraiyaraTurai sun sanarda rashin samun nasarar taronsu game da shirin nukiliya na Iran.

Ministocin harkokin wajen Jamus Frank Welter Steinmeier da takwaransa na Faransa Philippe Douste-Blazy sunce sun bukaci Iran data dakatar da bincikenta da ta koma akan sinadaren Uraniyum,wadda Iran din tayi watsi da shi.

A ranar litinin mai zuwa ne idan Allah ya kai mu hukumar kula da yaduwar nukiliya zata yanke shawara akan yiwuwar takunkumi akan kasar ta Iran.