1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwararar 'yan ci rani zuwa Ingila

Gazali Abdou TasawaAugust 28, 2015

Shugabanni a London na tunanin gabatar da sabbin dokoki na rage yawan 'yan gudun hijirar dake shiga kasar a wani adadi da ba a taba samun kamarsa ba

https://p.dw.com/p/1GNdH
Flüchtlinge in Calais Archiv 2013
Hoto: AFP/Getty Images/Philippe Huguen

A Ingila ba a taba samun wani lokaci da 'yan ci rani suka yi yawa, kuma suke ci gaba da kwarara a kasar kamar a wannan lokaci ba. Yawan 'yan ci rani da suka shiga kasar, idan aka dauke wadanda tuni suka fice daga cikinta karkashin matsin lamba, sun kai adadin dubu 330 tsakanin shekara ta 2014 zuwa 2015, abin da ya zama karin mutane dubu 94 kenan idan aka kwatanta da na shekara ta 2013. Musamman kididdiga ta nuna cewar 'yan ci rani da suka shiga Ingila a tsakanin wannan lokaci sun karu, inda mafi yawansu suka fito daga Poland, yayin da ake samun karuwar 'yan ci rani daga kasashen Romaniya da Bulgariya dake shiga Ingila din suna neman aikin yi, tun da aka bude iyakokin wadannan kasashe bayan sun shiga Kungiyar Hadin kan Turai.

Damuwar gwamnati kan adadin 'yan ci rani a Ingila

England Birmingham Premierminister David Cameron
Hoto: picture alliance/empics/P. Ellis

Gwamnmatin Ingila mai ra'ayin 'yan mazan jiya, ta baiyana rashin jin dadinta a game da wannan adadi, saboda shekaru hudu da suka wuce, Firaminista David Cameron yayi alkawarin cewar zai rage yawan dubban 'yan ci rani dake shigar kasar.

"Yace idan muka aiwatar da matakan da muka sanar dasu a yau, kuma muka yi nazarin dukkanin fannonin da suka shafi kaurar jama'a masu shigowa kasarmu ta hanyoyin halaliya da bakin haure, to kuwa yawan 'yan ci ranin ya na iya raguwa zuwa matsayin da yake a shekaru na 80 da shekaru na 90, lokacin da batun ci rani ba ya kan gaba a jerin al'amura na siyasa. Na kuma yi imanin hakan ya na nufin yawan 'yan ci rani dake shigowa kasarmu a ko wace shekara ba za su wuce dubbai gwammai ba, maimakon tun daga shekaru goman da suka wuce ba".

To sai dai wannan hangen nesa da Cameron ya yi bai tabbata a zahiri ba. Hakan ma shi ya sanya sakataren Ingila mai kula da al'amuran baki James Brokenshire tilas ya amince da gaskiyar cewar yadda aka so ba haka ya samu a zahiri ba game da kwararar 'yan ci rani cikin kasar.

Sabbin alkaluma game da kwararar 'yan ci rani daga kasashen Kungiyar Hadin kan Turai, za su kara tsananta muhawara a kasar game da ci gaba da kasancewarta a wannan kungiya, musamman saboda Ingila din ta nuna tantama ko rashin gamsuwarta da tsarin nan na bai wa ma'aikata daga kasashn Kungiyar Hadin kan Turai 'yancin shiga duk kasar da suke so su yi aiki. Dangane da haka ne masu adawa wakilcin ta a kungiyar suke ganin dacewar ficewarta, yadda Ingila din za ta sami 'yancin daidaita batun yan ci rani yadda zai dace da bukatunta. Dan majalisar dokoki Pater Bone na jam'iyar Conservative, ya ce idan har aka kawo karshen tsarin na 'yancin yan kasashen Turai na samun aiki a duk inda suke so, ya yi imanin idan aka zo zaben jin ra'ayi kan ci gaba da zaman Ingila a kungiyar a shekara ta 2017, 'yan Ingila za su goyi bayan ta ci gaba da zama a cikinta.

Mahawara kasashen Turai kan matsalar 'yan ci rani

To sai dai hukumar Kungiyar Hadin kan Turai da ita ma gwamnatin Jamus sun nuna cewar babu wani abin da zai taba tsarin na bai wa 'yan kungiyar EU damar zuwa kasar da suke so domin neman aiki. Su ma kamfanoni da masana'antun Ingila suna son ci gaba da wannan tsari, kamar yadda Mike hawes shugaban kungiyar masana'antun kera motoci a Ingila ya nunar.

Angela Merkel beim EU-Gipfel
Hoto: Reuters/P. Wojazer

"Ya ce mun ji ra'ayoyin wakilanmu, a tambayoyin da muka yi bara, inda suka ce suna son ci gaba da zama a Kungiyar Hadin kan Turai, suna kuma bukatar cigaba da tsarin bai wa 'yan kungiyar damar shiga kasar da suke so domin samun aikin yi. A masana'antun kera motoci suna fama da matsalar karancin kwararrun ma'aikata. Muna neman kwararrun injiniyoyi ruwa ya jallo a dukkanin Nahiar Turai, domin cike gibin da muke da shi a nan Ingila".

Sabbin alkaluma sun kuma tabbatarda cewar Ingila 'yan gudun hijiran da ta karba basu da yawa idan aka kwatanta da Jamus. Kashi hudu cikin darine kawai na 'yan ci ranin suke zaman 'yan gudun hijira, saboda Ingila din ta ki yarda a tsara wa ko wace kasa kason 'yan gudun hijira da za ta karba a cikinta.