1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

031110 D Türkische Auswanderer

November 3, 2010

Dubban ƙwararrun Jamusawa masu asali daga Tukiya sun fara kwarara zuwa ƙasarsu tasu ta asali.

https://p.dw.com/p/PxhJ
Turkawa 'yan kaka gida a Jamus.Hoto: AP

Dubban Jamusawa 'yan asalin Turkiya sun fara ƙaura zuwa ƙasar tasu ta asali duk da ƙwarewa ta sana'o'i da kuma ta harshen Jamusaci da suke da ita. Suna yin hakan kuwa saboda kyakyawar damar da suke da ita a can Turkiyar.

Emine Sahin dai na zaman wakiliyar waɗanda suke ƙaura zuwa ƙasar ta Turkiya. An haife ta ne a birnin Ankara na ƙasar ta Turkiya. An kuma zo da ita Jamus ne a lokacin da take 'yar jaririya. Daga nan ne ta shiga makaranta inda ta yi karatu har ya zuwa matsayin jami'a. Tana kuma riƙe ne da fasfo na Jamus da kuma na Turkiya.

Ta ce "Suna na Emine Sahin ina da shekaru 38 . Sana'ata ita ce tsara gine-gine kuma na zo ne daga birnin Frankfurt na ƙasar Jamus.Shekaru huɗu kenan da nike zaune nan Turkiya. Shekaru biyu kenan kuma da nike zaune a Istanbul bayan da na yi zama a garin Izmir."

A shekarar 2003 ne ta gama karatun jami'a. Shekaru uku bayan haka ne kuma ta tsai da shawara yin balaguro zuwa Turkiya.

To sai dai babu wani banbancin da ke akwai tsakanin kai ziyara da ƙaura zuwa gida, ko kuma kasancewa ɗan ƙasar Turkiya da kuma Bajamashe mai asali daga Turkiya. Abubuwa guda biyu ne dai ke da alaƙa da juna: Na farko shi ne samun asali daga Turkiya na biyun kuma lokaci yin kaka gida a Jamus. Shekaru huɗu kenan da Emine Sahin ta bar Jamus ta koma Turkiya inda yanzu take aiki a matsayin shugaban ma'aikatar gine-gine. Ta tsai da shawarar yin hakan ne daga sama, bayan da ta yi asarar gurbin aikinta a birnin Frankfurt.

" Na tsai da shawarar zuwa Turkiya ne domin na je na shaƙata . Bayan da muka yi zama na watanni biyu ne dai, ni da iyaye na mu kai tsai da shawarar ci gaba da zama a Turkiya saboda cewa na gano wata gagarumar dama da zan samu."

Cigdem Akkaya na ɗaya daga cikin waɗanda suka ƙaura zuwa ƙasar ta Turkiya. Ko kafin ta koma gida Turkiya ta shafe shekaru 15 tana jagorantar cibiyar nazari akan Turkiya a nan Jamus. A yanzu tana shugabancin wata ma'aikata ta tsara yin hulɗa da jama'a da kuma bukukuwa. Amma a duk lokacin hutunta ta kan gayyaci dukan waɗanda suka koma gida daga Jamus domin nishaɗartar da su. Da farko mutane da ke halartan nishadin ba su zarta 20 ba. Amma a yanzu Cigdem Akkaya tana tura gayyata ga mutane sama da dubu guda, ta hanyar waya. To sai dai a cewar Akkaya akwai wasu da ke tsintar kansu cikin mawuyacin hali bayan dawowrsu daga Jamus.

"A haƙiƙa ana fuskantar mawuyacin hali saboda cewa sanin harshen Jamusanci ko kuma shahadar karatun jami'a a Jamus kaɗai ba za su wadatar ba. Dalilin haka kuwa shine masana'antun Turkiya suna buƙatar mutane masu kwarewa ne daga sassan daban-daban na duniya, amma ba daga Jamus kaɗai ba."

Orkide Sulun wadda malama ce mai shekaru 27 na ɗaya daga cikin waɗannan mutane. A dai halin da ake ciki yanzu tana shan fama wajen samun aikin yi a birnin Istanbul.

Mawallafi: Steffen Wurzel/ Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmad Tijani Lawal