1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwararar baƙin haure a ƙasar Spain

ƙasashen Spain da Mauritaniya sun sanya hannu a kan wata yarjejeniya ta daƙile kwararar baƙin haure zuwa ƙasar Spain. Yarjejeniyar ta haɗa da tasa ƙeyar mutanen da aka kama da laifi domin maida su zuwa ƙasashen su na asali tare kuma da magance matsaloli na safarar mutane. Yarjejeniyar ta zo ne a daidai lokacin da wasu baƙin hauren su kimanin 294 suka isa tsibirin Canary na ƙasar Spain a ranar Talata. A wannan shekarar baƙin haure kimanin 24,000 ne suka shiga ƙasar ta Spain, adadin da ya ninka har sau uku fiye da yan shekarun baya.