1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake samun wanda aya kamu da Ebola a Kwango

Abdul-raheem Hassan MNA
May 14, 2018

A karshen makon ne hukumomin kiwon lafiya suka tabbatar da samun labarin mutumin da ya sake kamuwa da cuta a arewa maso yammacin Kwango.

https://p.dw.com/p/2xgyP
ARCHIV Ebola-Ausbruch in Liberia 2014
Hoto: picture alliance/AP Photo/J. Delay

Jami'an kiwon lafiya na Majalisar Dinkin Duniya na shirin kaddamar da ayyukan gaggawa na allurar rigakafi daga cutar Ebola, bayan da aka sake samun tabbacin barkewarta a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango.

A cewar hukumar lafiya ta duniya wato WHO, kawo yanzu mutane 18 ne suka mutu daga cutar, yayin da ake fargabar wasu 35 da kamuwa da cutar.

A wannan mako ne hukumar za ta fara allurar rigakafi a kan iyakar kasar da sauran kasashe makotanta.