Kwango: Juyayin rashin madugun adawa | Siyasa | DW | 02.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kwango: Juyayin rashin madugun adawa

Mutane na ci gaba da nuna juyayinsu bisa rasuwar madugun 'yan adawar kasar Kwango Etienne Tshisekedi wanda ya rasu a wani asibiti da ke kasar Beljiyam inda ya yi gajeriyar jinya.

Allah ya yi wa babban dan adawan nan na kasar Kwango Etienne Tshisekedi rasuwa a wani asibiti da ke birnin Brussels na kasar Beljiyam. Marigayin ya dawo karsar ta Beljiyam ne bayan komawarsa kasar Kwango a watan Yulin da ya gabata lokacin da jikinsa ya yi tsanani.  Kama daga birnin Brussels inda ya rasu, zuwa kasarsa ta haihuwa, mutane na ci gaba da nuna juyayinsu dangane da rasuwarsa. Lokacin da aka samu labarin mutuwarsa, da dama daga cikin 'yan kasar ta Kwango sun je har asibitin Sarauniya Elizabet inda ya rasu don nuna alhininsu.

Demokratische Republik Kongo Etienne Tshisekedi gestorben (Reuters/F. O'Reilly)

Marigayi Tshisekedi fitaccen mai adawa da tazarcen shugaban Kwango Joseph Kabila ne

 Kamar yadda magoya bayansa ke kiran shi, ya mutu ne ya na da shekaru 84 a duniya kuma ya yi suna sanadiyyar gwagwarmaya da ya yi tun a lokacin mulkin tsohon dan kama karya Mobutu Seseseko wanda suka yi aiki tare kafin ya juya ya zama dan adawa a kasar. Labarin mutuwar ta sa dai ta girgiza al'ummar kasar Kwango inda rahotanni ke cewar mutane da dama na zaman makoki na musamman.

An dai haifi Etienne Tshisekedi ne a ranar 14 ga watan Disamba na 1932 a garin Kananga na jihar Kasai da ke tsakiyar kasar Kwangon. An kuma nada shi mataimakin kwamishinan shari'a na gwamnatin rikon kwaryar kasar a wannan lokaci, kuma a shekara ta 1961 ya samu digiri na uku a fannin shari'a.  A shekarar 1992 ce ya zama firaminista, sai dai bai jima kan mukamin ba don a shekara ta 1997 ya bar wannan matsayi bayan da Laurent-Désiré Kabila ya kifar da gwamnatin Shugaba Mobutu.

Marigayin wanda ya mutu sakamakon cuta mai nasaba da huhu, ya bar kasarsa ta kwango ne a ranar 24 ga watan Janairu da ta gabata a daidai lokacin da jam'iyyarsa ta UDPS da sauran 'yan adawan kasar ta Kwango ke neman mafita ga rikicin siyasar kasar sakamakon kin saukar da shugaba Joseph Kabila ya yi a karshen wa'adin mulkinsa na ranar 19 ga watan Disamban bara.

Sauti da bidiyo akan labarin