1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Kwango ta shiga tsaka mai wuya

Abdullahi Tanko Bala
January 4, 2018

A Jamhuriyar demokradiyyar Kwango, zanga-zangar adawa da gwamnati ta sauya salo, inda babban coci mafi tasiri a kasar wato cocin Katholika, ya mara baya ga boren da ake yi wa gwamnati.

https://p.dw.com/p/2qL29
DR Kongo Präsident Kabila einigt sich mit Opposition
Hoto: Getty Images/AFP/J. D. Kannah

A Jamhuriyar demokradiyyar Kwango, zanga-zangar adawa da gwamnati ta sauya salo, inda yanzu babban coci mafi tasiri a kasar wato cocin Katholika, ya mara baya ga boren da ake yi wa gwamnati. Don haka jam'iyar Adawa da Cocin Katholika, sun daura anniyar ganin bayan gwamnatin Joseph Kabila, wanda ya ki sauka duk da karewar wa'adin mulkinsa, inda ya yi fatali da yarjejeniyar da aka cimma.

Unruhen im Kongo
Hoto: Getty Images/AFP/J. Wessels

Dama dai Cocin na Katholika shi ne ya shiga tsakanin gwamnatin da 'yan adawa, lokacin da aka samu barakar bayan rashin shirya zabe, a lokacin an anmincewa shugaba Kabila ya ci gaba da jagorantar kasar har izuwa karshen watan Disamba, bayan kura ta lafa Joseph Kabila ya yi fatali da wannan yarjejeniyar. Grigo Jaecke shi ne jami'in Gidauniyar Konrad Adenauer a Kinshasa.
Wannan wani sabon babi ne na sauyi a bangaren mutanen da a da suke shiga tsakanin don warware matsalar. Domin a da jami'an cocin sun kansance 'yan ba ruwanmu. Daga bisani ne sukar gwamnatin ya kara yin karfi, Don haka babu wanda ya san inda za ta kaya bisa boren da aka faro a jajiberin sabuwar shekara, haka kuma babu tabbas ko gwamnatin ta shugaba Kabila za ta iya shawo kan lamarin.

Angola | Ankunft des kongolesischen Präsidenten Joseph Kabila bei einem meeting der süd- und zentralafrikanischen Staaten in Angola
Hoto: REUTERS/K. Katombe

A cewar masanin dai idan har gwamnatin Joseph Kabila ta dauki matakan rusa hukumar tafiyar da cocin kasar, to kuwa bore da kyamar gwamnatinsa za su yi matukar karuwa. Ko da yake tuni matsalar rayuwa ta yi tsanani a kasar tun a watannin baya. Talauci a Kwango ba zai misaltu ba, abinda ma ya kara tunzura jama'a don yiwa gwamnatin bore, bayan da shugaba Kabila yaki mutunta kundin tsarin mulki, ya turje sai ya zarce akan mulki.
Idan yanzu gwamnati ta fara tabo shugabannin cocin Katholika, Wace ke da matukar kima da martaba a idanun jama’ar kasar, kuma wadda ke da karfin fada a ji, to ina gani babu raba dayan biyu, jama'a za su juwa gwamnatin baya, inda watanni ko makwanni da ke tafe boren adawa da gwamnati zai yi matukar bazuwa

A kasar ta Kwango dai cocin Katholika na da matukar fada aji, wanda ya samo asali tun zamanin mulkin mallaka, inda turawa suka yi amfani da coci a matsayin wadda ke bayarda ilimi da kiwon lafiya da sauran ayyukan raya kasa. A yanzu da gwamnatin ta rasa tasirin yi wa jama'a aiki, Cocin ne kadai ke tallafawa jama'a wajen samar musu ababuwan more rayuwa, don haka wannan boren kyamar gwamnati da cocin katholika ta shiga, zai matukar raunana gwamnatin