1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: An bude wuta kan masu bore

Ahmed Salisu
February 25, 2018

Jami'an tsaro a birnin Kinshasa na Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo sun bude wuta kan masu zanga-zanga ta neman shugaban kasar Joseph Kabila  ya sauka daga mulki.

https://p.dw.com/p/2tJ9H
Proteste in Kinshasa Kongo
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

Wannan lamari da ya faru a birnin Kinshasa ya yi sanadin rasuwar mutum guda da kuma jikkata wasu mutane da dama. Wani jami'i a asibitin St Joseph de Limete da ke Kinshasa ya ce tun da misalin karfe bakwai na safiya suka fara karbar wanda aka raunata bayan da jami'an tsaro suka afkawa masu zanga-zangar wadda ake samun goyon bayan cocin Katolika na kasar.

Can ma a birnin Kisangani da ke arewa maso gabashin kasar akalla mutane biyu sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga kamar yadda wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP da ke birnin ya bayyana.

Tun a jiya ne dai hukumomi a kasar suka haramta yin dukannin wata zanga-zanga ko wani gangami sai dai wanda suka shirya wannan zanga-zanga ta yau sun yi wa wannan umarni kunnen kashi inda suka yi fitar dango kan tituna tare da rera kalamai na kin jinin Kabila da ma nema ya sauka daga mulki cikin hanzari.