1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwanaki uku bayan cafke tsohon shugaban kasar iraki da sojojin taron ...

December 16, 2003
https://p.dw.com/p/Bvn4
dangi sukayi a gidansa dake karkashin kasa kusa da kauyen tikrit a cikin kasar ta iraqi,wasu mutane masana masu kuma sharhi a jaridun kasar Jordan sun fito fili´inda suka shaidar da cewa babu tababa sojojin taron dan´gin sun kame Saddam din ne ta hanyar ba zata,musanmamma ta amfani da wasu sanadarai. Da farko dai masu sharhin sun habarta cewa kame Saddam Hussain da sojojin taron dangin sukayi ba tare da kace nace ba,wata babbar alama ce dake nunin cewa sunyi amfani da wata guba kafin cafke tsohon shugaban kasar ta iraqi,musammamma ganin irin halin da aka nuno shi a talabijin bayan kama shi. Bugu da kari masharhantan sun ci gaba da bayanin cewa,bisa irin halin da aka nuno tsohon shugaban kasar ta iraqi,tamkar kace ar ya zura a guje ko kuma tamkar kaza a hannun kuku,bayan kuma kowa a duniya ya yarda da cewa Saddam Hussain muzakkarin namiji ne,babu shakka a cewar jaridar ta Al hilal akwai alamun sojojin taron dangin sunyi amfani da iska mai guba wajen rikirkita tunanin sa kafin kamashi. A hannu daya wata diya ga Saddam Hussain wacce take gudun hijira a kasar ta Jordan mai suna Raghad cewa tayi babu shakka anyi amfani da wani sanadarin wajen cafke Saddam domin a cewarta ta san mahaifinta wajen nuna kwazo da kuma dauriya,wanda a don haka ba yadda zaayi ace an kama shi salin alin ba tare da an kai ruwa rana ba.

Ita kuwa Jaridar Al sabeeel,wacce itama a kasar ta Jordan ake bugata a kowane mako cewa tayi,akwai shakku dangane da hoton da aka nunawanda aka danganta shi da cewa Tsohon shugaban kasar ta iraqi ne,musammamma bisa laakari da irin kisisinar kasar Amurka. A wata sabuwa kuma daya daga cikin mutanen da suke shirin kafa kotun da zata tuhumi tsohon shugaban kasar ta iraqi, mai suna Dara Nooraldin ta tabbatar da cewa gurfanar da Saddam A gaban kuliya zai dauki watanni da dama masu zuwa,domin bawa wasu alkalai daga wasu kasashe damar sauraron karar.

Haka shima shugaban kasar Amurka wanda yake gudanar da murnar biki na biyu dangane da cafke tsohon shugaban kasar ta iraqi,ya shaidar da cewa kotun da zata tuhume shi zata,gabatar da aikin nata ne cikin gaskiya da kuma adalci. A kuwa ta bakin babban sakataren mdd Kofi Anan,cewa yayi ba zaiya da yankewa Saddam Hussain hukuncin kisa ba,sai dai wani hukuncin na daban. Ita kuwa Ragahad Diya ga Saddam Hussain A madadin iyalansa cewa tayi basa son a tuhumi Mahaifin nasu a wannan kotu ta musanmamman da za,a kafa a kasar ta iraqi,bisa rashin adalci da suke ganin za,a nuna mashi,a maimakon hakan cewa tayi kamata yayi a gurfanar dashi a gaban kotun kasa da kasa.

A wata sabuwa kuma da dama daga cikin mutanen duniya na tunanin yadda makomar kasar ta iraqi zata koma bayan kame tsohon shugaban kasar,musanmamma bisa laakari da irin halin da kasar take ciki a yanzu haka. Wannan hali kuwa a cewar rahotanni da suka iso mana baya rasa nasaba da tashe tashen bama bamai da kuma harin kwanton bauna dana sari ka noke da ake kaiwa kann sojojin taron dangin a fadin kasar baki daya. Bisa kuwa irin wannan hali manazarta abubuwan da kaje yazo a cikin alumma na masu raayin cewa, babu shakka har yanzu akwai sauran rina a kaba,sai dai kuma daman hausawa kance ko ana ruwan kibau mai rabon ganin badi sai ya gani.