KWANAKI DAYA BAYAN BAYYANAR SADDAM HUSSAIN A KOTU. | Siyasa | DW | 02.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

KWANAKI DAYA BAYAN BAYYANAR SADDAM HUSSAIN A KOTU.

HOTUN SADDAN YAYIN DAYA BAYYANA A KOTU A KARON FARKO TUN BAYAN HAMBARAR DA MULKIN SA.

default

Sakamakon bayyanawar tsohon shugaban kasar iraqi a wata kutu dake iraqi A yau juma,a da yawa daga cikin jaridun kasashen larabawa da yankin Asia sun mayar da hankaline wajen yin sharhi game da zaman kotun na jiya.

Rahotanni dai sun nunar cewa da yawa daga cikin wadan nan jaridu sun buga bayanan da saddam hussain ya fara yine a kotun kusa da wani Hoton sa yana saye da bakar kwat tare da farar riga a cikin ta.

Manya manyan batutuwan da wadan nan jaridu suka fi mayar da hankali kai shine Nine Saddam Hussain shugaban kasar iraqi. Wan nan kotu ba kotu bace illa dai kawai wani dandali na nuna wasan kwaikwayo. Ba nine na gudanar da miyagun laifuka na yaki ba illa shugaban Amurka Bush. Wadan nan kalaman na saddam Hussain sune abin da wadan nan jaridu sukafi yin sharhi a kann su.

A misali wadan nan jaridu na ganin cewa duk da irin halin da Saddam Hussain ya tsinci kansa a ciki har yanzu yana nan a kann bakan sa na cewa shine Shugaban kasar Iraqi. Ba a da bayan haka kuma Saddam Hussain na ganin cewa Babban mai laifi Shine Shugaba Bush amma bashi kann sa ba a don haka ya bayyana wan nan kotu da cewa bata da hurumin da zata tuhumeshi abin da tace tana zargin sa da aikatawa.

A waje daya kuma lauyoyin dake shirye shiryen fara kare Saddam Hussain a gaban kotu na ganin cewa an gudanar da rashin adalci a lokacin zaman kotun na jiya alhamis bisa kin barin lauyan Saddam ya zama yana kotun a wan nan lokaci.

Babban lauyan dake jagorantar tawagar lauyoyin da zasu kare Saddam Hussain wato Mohd Rashdan ya fadawa kamfanin dillancin labaru na AFP cewa wan nan kotu bata da hurumin gudanar da wan nan sharia domin kuwa an nada alkalan ne ba bisa kaida ba.

A takaice dai lauya Mohd ya soki lamirin tsohon shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar wato Paul Bremer da gudanar da wan nan makarkashiya bisa umarnin kasar Amurka kafin ficewar sa daga wan nan kasa.

Mohd Rashdan yaci gaba da cewa a yanzu haka suna fuskantar barazana daga gwamnatin rikon kwarya ta iraq bisa wan nan aiki da suke shirye shiryen farawa. Bisa hakan a cewar shugaban tawagar lauyoyin tuni suka aike da takardar neman goyon bayan amincewar wasu kasashe na duniya ciki har da kasar faransa na tabbatar da tsaron su a iraqi a lokacin wan nan gagarumin aiki kafin su shiga kasar ta iraqi tukuna.

Shi kuwa Mr Ziad daya daga cikin wadan nan lauyoyi da zasu kare Saddam Hussain din cewa yayi bayanan da Saddam Hussain yayi a jiya bayanai ne da suka ruda shi kansa alkalin kotun domin ya san abin da yake wanda hakane ma yaki sa hannu akan zarge zargen da ake masa har sai idan da yardar lauyoyin sa.

A daya hannun kuma mahukuntan Amurka sun shaidar da cewa suna nan suna har hada bayanai na shaida da zasu gabatar a zaman wan nan kotu na gaba don tabbatar da cewa Saddam Hussain ya aikata ire iren laifuffukan da ake zargin sa da aikatawa.

A waje daya kuma a cewar ministan sharia na kasar ta iraqi Malek Al hassan matukar wan nan kotu ta kama Saddam Hussain da wadan nan laifuka bakwai da ake zargin sa da aikatawa to babu shakka hukuncin kisa zai hau kansa.

Daga cikin abubuwa bakwai da ake zargin Saddam Hussain bakwai akwai yakin daya farwa kasar kuwait a shekara ta 1990 da kisan shugabannin addinai daya dinga yi a tsawon mulkin sa da kisan daya dinga sawa ayiwa yan kabilar kurdawa dake wan nan kasa ta hanyar amfani da hodar ibilis.

Ibrahim Sani