Kwanaki dari da kafa gwamnatin hadaka a Jamus | Labarai | DW | 22.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwanaki dari da kafa gwamnatin hadaka a Jamus

Zauren taro tsakanin CDU/CSU da SPD

Zauren taro tsakanin CDU/CSU da SPD

Jam´iyyun CDU da CSU da kuma SPD ,a nan Jamus sun yaba da irin ci gaban da suka samu a gwamnatance kwanaki 100, bayan sun kafa gwamnati.

A cewar shugaban jam´iyyar ta CDU a majalisar dokokin kasar wato Volker Kauder, gwamnatin hadakar ta samu warware matsaloli da daman gaske dake ciwa kasar tuwo a kwarya a tsawon wannan gajeren lokaci

.Daga cikin wadannan matsaloli kuwa a cewar shugaban akwai shirin nan na yuro biliyan 25 da aka cimma matsaya a kansa, wanda zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da kuma rage yawan marasa aikin yi a kasar.

Shi kuwa, shugaban jam´iyyar SPD a majalisar dokokin , wato Peter Struck cewa yayi babban abu da za´a yaba dashi a tsawon lokacin , shine na aiki a tsakanin jamiyyun bisa fuskantar juna.

Bisa kuwa irin yadda rawar ta kasance a tsawon wadannan kwanaki, Mr Peter Struck yace da alama gwamnatin zata samu galabar samo bakin zaren inganta fannin harkokin lafiya na kasar, ta hanyar gudanar da wasu sabbin sauye sauye.