1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwan gaba- kwan bayan harkokin siyasa a Libanon

Ibrahim SaniNovember 24, 2007
https://p.dw.com/p/CSdw

Wa´adin shugaban ƙasar Libanon, Mr Emile Lahoud ya ƙare ba tare da zaɓar wanda zai maye gurbinsa ba. Hakan dai ya biyo bayan rashin fuskantar juna ne, a tsakanin ´ Yan majalisar dokokin ƙasar. Wannan giɓi dai ya farune sakamakon ƙauracewa zaman Majalisar da wasu daga cikin su su ka yi ne. Rahotanni sun nunar da cewa ´Yan Majalisar da su ka ƙauracewa zauren a jiya na daga cikin ma su goyon bayan ƙasar Syria ne. Tuni dai Mr Emile Lahoud ya mika ragamar tafiyar da ofishinsa ga hannun sojin ƙasar, bayan ƙarewar wa´adin mulkin sa a jiy. To sai dai Faraminista Fuad Siniora ya ce hakan ya saɓa da tsarin kundin mulkin ƙasar. A mako mai zuwa ne ake sa ran ´Yan Majalisar za su ƙara zama, domin shawo kann rikicin siyasar ƙasar.