Kwamitin ´yan majalisar dattijan Amirka ya yi fatali da shirin Bush | Labarai | DW | 25.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwamitin ´yan majalisar dattijan Amirka ya yi fatali da shirin Bush

Kwamitin dake kula da harkokin waje na majalisar dattijan Amirka ya yi watsi da shirin shugaba GWB na tura karin dakaru zuwa Iraqi. A kuri´ar da membobin kwamitin suka kada, wakilai 12 daga cikin 21 sun nuna amincewar su da wani kuduri wanda ya bayana sabon shirin na Bush da cewa babban koma baya ne ga bukatun kasar. Maimakon haka kwamitin yayi kira da sannu a hankali a fara mikawa gwamnatin Iraqi ragamar tsaron kasar. An kada kuri´ar ne kwana guda bayan kiran da Bush ya yiwa ´yan majalisun dokokin na su marawa sabon shirin sa dangane da Iraqi baya.