Kwamitin sulhun MDD ya yi tir da kisan da aka yiwa Gemayel a Libanon | Labarai | DW | 22.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwamitin sulhun MDD ya yi tir da kisan da aka yiwa Gemayel a Libanon

Tarzoma ta barke a Libanon bayan kisan gillan da aka yiwa dan siasar kasar mai sukar lamirin Syria kuma ministan masana´antu Pierre Gemayel. Rahotanni sun shaidar da cewa an bankawa motocin masu goyon bayan Syria wuta. Da farko ba tare da wata rufa-rufa ba, kwamitin sulhun MDD yayi Allah wadai da kisan da aka yiwa ministan masana´antu na Lebanon Pierre Gemayel, sannan a lokaci daya kwamitin sulhun yayi kira ga ´yan kasar ta Lebanon da ma al´umar yankin baki daya da su nuna juriya. A cikin wata sanarwa da Faransa ta tsara, membobi 15 na kwamitin sulhun sun bayyana dan siyasar wanda kirsta ne da cewa mai kishin kasa ne wanda ya kasance wata alamar wanzuwar ´yancin siyasa a kasar ta Lebanon. Shi kuwa shugaban Amirka GWB ya yi tir da kisan sannan ya zargi Syria da Iran da kokarin yiwa gwamnatin FM Fuad Siniora yankan baya.