Kwamitin sulhu ya yi tir da harin da aka kai kan sojojin AU a Darfur | Labarai | DW | 03.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwamitin sulhu ya yi tir da harin da aka kai kan sojojin AU a Darfur

Kwamitin sulhu na MDD ya yi tir da mummunan harin nan na karshen mako wanda ya halaka sojoji 10 na rundunar kiyaye zaman lafiya ta KTA AU a lardin Darfur na kasar Sudan. Bayan wata tattaunawa ta kwanaki biyu, jakadan Ghana a MDD Leslie Christian wanda ke jagorantar kwamitin sulhu a wannan wata ya karanta wata sanarwar wadda ta yi tir da harin wanda ake zargin ´yan tawaye da hannu a ciki. MDD ta bukaci a yi duk iya kokarin cafke wadanda suka aikata wannan ta´asa don a gurfanad da su gaban shari´a. Kwamitin sulhu mai membobi kasashe 15 ya ce harin ya zo ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da taron sulhu a Libya a ranar 27 ga watan nan na oktoba. Yayi gargadin cewa ba za´a amince da duk wani yunkuri na yiwa kokarin samar da zaman lafiya a Darfur yankan baya ba.