Kwamitin Sulhu ya yi tir da furucin shugaba Ahmedi Nejad na kyamar Isra´ila | Labarai | DW | 29.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwamitin Sulhu ya yi tir da furucin shugaba Ahmedi Nejad na kyamar Isra´ila

Kwamitin sulhu na MDD yayi Allah wadai da kalaman da shugaban Iran Mahmud Ahmedi Nijad yayi na nuna kyamar Isra´ila. A cikin wani kuduri da ya zartas, kwamitin sulhu yayi kira ga dukkan kasashen membobin MDD da su guji yin kalamai ko wasu abubuwan masu yin barazana ga ´yancin wanzuwar wata kasa. Jakadan Isra´ila a MDD Dan Gillermann yayi maraba da kudurin. A ranar laraba da ta wuce shugaba Ahmedi Nijad yayi kira da a share Isra´ila daga taswirar duniya. A jiya juma´a dubun dubatan mutane a Iran sun halarci zanga-zangar nuna kyama ga Isra´ila. Ko da yake a kowace shekara tun bayan juyin juya halin Islama a Iran a cikin shekarar 1979, hukumomi ke shirya taron gangami da aka yiwa lakabi da ranar Birnin Kudus, to amma taron na jiya ya samu karbuwa kwarai da gaske musamman saboda kalaman nuna kyamar Isra´ila da shugaba Ahmedi Nijad yayi.