Kwamitin Sulhu ya amince da wani kuduri kan Iran | Labarai | DW | 29.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwamitin Sulhu ya amince da wani kuduri kan Iran

A takaddamar da ake yi akan shirin nukiliyar Iran, membobin dindindin guda biyar na kwamitin sulhun MDD da kuma Jamus sun amince da wani kuduri akan gwamnatin Teheran. Ana sa ran cewa a cikin mako mai zuwa kwamitin sulhun zai kada kuri´a akan kudurin. Bayan haka za´a ba Iran wa´adin zuwa karshen watan agusta da ta dakatar da shirin inganta sinadarin uranium kana kuma ta bi dukkan ka´idojin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya. Idan ta ki yin haka, to ana iya kakaba mata takunkumi, wanda dole sai kwamitin sulhun ya amince da shi a cikin wani sabon kuduri. Rasha da China sun ki amincewa MDD ta dauki matakan jan kunnen Iran a yanzu.