1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwamitin Sulhu ya amince da wani kuduri da ya yi Allah wadai da halin da ake ciki a Burundi

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi tir da tashin hankalin da ake samu a Burundi wanda ya janyo mutuwar mutane 250.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudirin da yi tir da tashe-tashen hankula da ake samu a kasar Burundi.

Fiye da mutane 250 suka hallaka tun daga watan Afrilu lokacin da Shugaba Pierre Nkurunziza ya kaddamar da neman wa'adin mulki na uku domin tsawaita mulkinsa. Kudirin ya nemi ganin an fara tattaunawa domin kawo karshen rikicin, tare da nuna yuwuwar tura dakarun kiyaye zaman lafiya.

Francois Delattre ke zama jakadan Faransa na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya ce za a yi duk abin da ya dace domin kauce wa makamancin rikicin da ya faru a Ruwanda cikin shekarar 1994.

"Wannan kudiri ya kuma tura sako kan kawo karshe tashe-tashen hankula saboda jawabai na kiyayya. Kwamitin Sulhu zai yi abin da ke yuwuwa karkashin ikonsa domin kare kasar tsanduma rikici."