Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da tura Karin dakarun kare zaman lafiya zuwa Côte d’Ivoire. | Labarai | DW | 06.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da tura Karin dakarun kare zaman lafiya zuwa Côte d’Ivoire.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da tura wani rukuni na dakarun kare zaman lafiyanta da ke girke a Laberiya zuwa maKwabciyar Kasa ta Côte d’Ivoire. Dakarun dai za su kasance a Côte d’Ivoire din ne har zuwa Krashen watan Maris mai zuwa, inda za su Karfafa wa takkwarorinsu da ke can gwiwa

Wani jami’in diplomasiyya, ya fada wa maneman labarai cewa rukunin zai Kunshi dakaru dari biyu ne daga N ajeriya, tare da motoci masu sulke 14 da Kananan motoci 18, wadanda a halin yanzu ke tare da rundunar kare zaman lafiya ta Majalisar a Kasar Laberiya.