1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da tura Karin dakarun kare zaman lafiya zuwa Côte d’Ivoire.

February 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bv99

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da tura wani rukuni na dakarun kare zaman lafiyanta da ke girke a Laberiya zuwa maKwabciyar Kasa ta Côte d’Ivoire. Dakarun dai za su kasance a Côte d’Ivoire din ne har zuwa Krashen watan Maris mai zuwa, inda za su Karfafa wa takkwarorinsu da ke can gwiwa

Wani jami’in diplomasiyya, ya fada wa maneman labarai cewa rukunin zai Kunshi dakaru dari biyu ne daga N ajeriya, tare da motoci masu sulke 14 da Kananan motoci 18, wadanda a halin yanzu ke tare da rundunar kare zaman lafiya ta Majalisar a Kasar Laberiya.