1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kammala taro kan Korea Ta Arewa ba tare da cim ma daidaito ba.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kammala wani taro don tattauna matakan da za a ɗauka kan Korea Ta Arewa, saboda gwajin makaman nukiliyan da ta yi. Amma rahotanni sun ce an tashi taron ne ba da cim ma wata yarjejeniya ba. Japan da Amirka, na ƙoƙarin ganin cewa an ɗau tsauraran matakai ne kan Kora Ta Arewan, tare da yin matashiya da babi na 7 na tsarin kundin Majalisar Ɗinkin Duniyar, wanda ya ba da damar yin amfani da ƙarfin soji a kan duk mai take ƙudurin da aka zartar. Amma Sin ta bayyana cewa, ba za ta goyi bayan takunkumin da zai haɗa da yin amfani da ƙarfin soji ba. Su ko mahukuntan ƙasar ta Korea Ta Arewa, sun bayyana cewa za su ɗau duk wani takunkumi ne tamkar ƙaddamar da yaƙi kan ƙasar.

A halin da ake ciki dai, babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniyar, Kofi Annan, ya yi kira ga mahukuntan birnin Pyongyang da su yi taka tsantsan. A yau ne dai kwamitin sulhun zai sake zama don ƙoƙarin cim ma daidaito kan matakan da za a ɗauka.