Kwamitin Sulhu gaba daya ya goyi bayan Ban Ki-Moon don ya gaji mista Annan | Labarai | DW | 03.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwamitin Sulhu gaba daya ya goyi bayan Ban Ki-Moon don ya gaji mista Annan

Ministan harkokin wajen kasar Koriya Ta Kudu Ban Ki-Moon na kara samun goyon baya a matsayin mutumin da zai gaji babban sakataren MDD Kofi Annan. Daga cikin ´yan takara 6 dake neman wannan kujera ta sakatare janar na MDD, Mista Ki-Moon ne kadai bai fuskanci wata adawa a wata kuri´a ta bayan fage da aka kada a kwamitin sulhu. Jim kadan bayan ba da sakamakon kuri´ar, dan kasar Indiya kuma mataimakin babban sakataren MDD dake kula da harkokin yada labaru, Shashi Tharoor ya ba da sanarwar janyewa daga takarar duk da cewa shi ya zo na biyu a kuri´u har sau hudu da aka kadan. Jakadan China MDD Wang Guangya ya tofa albarkacin bakinsa akan zaban na Ki-Moon, inda yace:

“Daga yau ya fito fili cewa minista Ban Ki-Moon ne dan takarar da kwamitin sulhu zai gabatar da sunansa ga babbar mashawartar MDD.”

A ranar 9 ga watannan na oktoba kwamitin sulhu zai kada kuri´a a hukumance don zaban sabon sakatare janar wanda zai kasance na 9 tun bayan kafuwar MDD kimanin shekaru 60 da suka wuce. Bayan nan babbar mashawartar majalisar mai kasashe memebobi 192 zata amince da mutumin da aka zaban.