1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwamitin Mdd zai zauna akan rikicin yankin Darfur

A wani lokaci ne a yau, kwamitin kula da hukumar kare hakkin bil adama na Mdd, zai gudanar da wani taro akan kasar Sudan.

Taron, wanda za a gudanar a birnin Geneva kuma ke a matsayin irin sa na farko, zai duba irin zarge zargen take hakkin bil adama ne a yankin Darfur na kasar Sudan.

Daukar wannan mataki dai da alama ya biyo bayan kiraye kirayen yin hakan ne daga kungiyoyin kare hakkin bil adama, a sabili da irin yadda ake ci gaba da take hakkokin yan adam a yankin.

Gudanar da wannan taro dai yazo ne a dai dai da lokacin da kasashen yamma ke matsawa kasar ta Sudan lamba,data yarda da zuwan dakarun sojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar.

Rahotanni dai sun rawaito sakataren Mdd Mr Kofi Anan na cewa akwai mummunan take hakkin bil adama a yankin na Darfur.