Kwamandan kungiyyar Hamas ya rasa ransa
March 31, 2006Talla
Daya daga cikin manya manyan kwamandojin kungiyar Hamas ta masu tsattsauran ra´ayi dake yankin Palasdinawa ya rasa ransa.
Hakan kuwa ya faru ne bayan da wasu abubuwa da suka fashe suka tashi da motar da yake a cikin ta.
Ya zuwa yanzu dai babu tabbas ko hakan nada nasaba da wani hari da dakarun sojin Israela suka kai a zigin gaza, to sai dai tuni mahukuntan kasar suka nesanta kann su da faruwar al´amarin.
Wannan al´amari dai ya faru ne kwana daya , bayan da wani dan kunar bakin wake daga yankin Palasdinawa yayi sanadiyyar rasuwar bani yahudu guda hudu a can yammacin kogin Jordan.
Tuni dai shugaban yankin na Palasdinawa, Mahmud Abbas, wanda ke ziyarar aiki a Africa ta kudu a yanzu yayi Allah wadai da faruwar wannan al´amari.