Kwalara a Zimbabwe | Siyasa | DW | 11.12.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kwalara a Zimbabwe

Ana ƙara yin kira ga shugaba Robert Mugabe da ya sauka daga kan karagar mulki sakamakon annobar cutar kwalara a ƙasarsa.

default

Annobar cutar kwalara a Zimbabwe

Halin da ake ciki a Zimbabwe sai ƙara taɓarɓarewa yake yi, inda yanzu haka tattalin arzikin ƙasar da tsarin kiwon lafiyarta suka ruguje kwata-kwata. Sama da mutane dubu 60 a ƙasar sun kamu da cutar kwalara sannan asusun UNICEF ya yi gargaɗin cewa yawan waɗanda cutar za ta yi ajalinsu yana iya haura mutane dubu biyu da ɗari biyar. Saboda haka shugabannin ƙasashen duniya suka fara ɗaga murya don neman shugaba Robert Mugabe da ya sauka. Su ma ´yan siyasa a Jamus sun yi maraba da sukar lamirin shugaba Mugabe da yanzu aka fito fili ana yi.

Ra´ayin ƙasashen yamma ya zo ɗaya cewa ya zama dole a ɗauki mataki dangane da mawuyacin hali da ƙasar Zimbabwe ta faɗa ciki. To sai dai ganin yadda tattalin arzikin ƙasar ya taɓarɓare, duk wani ƙarin takunkumi da za´a sanya mata ba zai yi ma´ana ba. Saboda haka yanzu Amirka da ministocin harkokin wajen ƙasashen tarayyar Turai suka yi kira ga shugaba Robert Mugabe mai shekaru 84 da ya sauka daga kan karagar mulki.

Jamus ta yi maraba da fitowa fili ana sukar lamirin gwamnatin Robert Mugabe. To sai dai da farko kamata yayi ƙasashen Afirka musamman maƙwabciyar Zimbabwe wato Afirka ta Kudu, su ƙara matsa lamba kan Zimbabwe inji Gert Weisskirchen kakakin jam´iyar SPD dake cikin gwamnatin ƙawance akan harkokin ta na ƙetare. Ya ce Jamus da sauran ƙasashen Turai za su mara musu baya.

Ya ce: "Mun nunawa Afirka Ta Kudu a fili cewa za mu yi iya ƙoƙarin mu don Afirka Ta Kudu kanta da ma yankin su kasance cikin shirin kafa gwamnatin wucin gadi har izuwa ga girke demoƙuraɗiyya a Zimbabwe nan ba da daɗewa ba kamar yadda muke fata. A nan kuwa Afirka ta Kudu za ta taka muhimmiyar rawa. A shirye muke mu taimaka idan Afirka Ta Kudu ta so haka."

Masu lura da al´amuran yau da kullum kan manufofin ƙetare sun ce a cikin ƙungiyar EU ana ƙara tattaunawa game da yiwuwar amfani da soji akan Zimbabwe musamman don rage raɗaɗin halin ƙaƙanikayi da al´umar ƙasar suka tsincin kansu ciki sakamakon ɓarkewar cutar kwalara. To sai dai wakilin jam´iyar ´yan ra´ayin gurguzu a majalisar dokokin Jamus Norman Paech yayi gargaɗi game da ɗaukar irin wannan mataki.

Ya ce: "Idan za mu kyale kowace ƙasa ta yanke shawara dangane da inda ake fama da bala´i na ɗan Adam ko inda za ta iya kai hari to kenan ƙudurorin Majalisar Ɗinkin Duniya da ma Majalisar kanta ba su da wani amfani."

Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ne kaɗai zai iya yanke shawara game da matakin da ya kamata a ɗauka kan Zimbabwe. Kafin ya yi haka dole Jamus da sauran ƙasashen yamma su ci-gaba da ba da taimakon jin ƙai da ake matuƙar buƙata a Zimbabwe. ´Yan siyasa a Jamus na fatan cewa matsin lamba daga ´yan siyasan yamma zai angiza ƙasashen Afirka da su ɗauki mataki mafi dacewa. Kawo yanzu dai ƙungiyar tarayyar Afirka da kuma ƙasar Afirka ta Kudu sun fito ƙarara sun nuna adawa ga kiraye-kirayen ga shugaba Mugabe ya sauka ko yin katsalandan a Zimbabwe.

A dai halin da ake ciki shugaban na Zimbabwe ya ce an daƙile annobar kwalarar a ƙasarsa. To sai dai sa´o´i ƙalilan gabanin wannan sanarwar Afirka Ta Kudu ta bayyana kan iyakarta da Zimbabwe a matsayin yankin da bala´i ya afka ma.

Sauti da bidiyo akan labarin