Kwalambiya: ′Yan tawayen ELN sun sako dan majalisa | Labarai | DW | 02.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwalambiya: 'Yan tawayen ELN sun sako dan majalisa

Kungiyar 'yan tawayen ELN a Kwalambiya ta sanar da sako a wannan Alhamis tsohon dan majalisar nan na kasar Odin Sanchez wanda take garkuwa da shi yau kusan watanni goma.

Sakin tsohon dan majalisar Odin Sanchez mai shekaru 61 na daga cikin sharuddan da dama gwamnatin Kwalambiyar ta gindaya wa kungiyar tawayen kafin soma duk wata tattaunawa. Sai dai a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter Kungiyar tawayen ta ELN ta ce a yanzu ya rage ga gwamnatin kasar ta Kwalambiya da ta cika alkawarin da ta dauka na yin afuwa ga wasu kumandojinta biyu da ake tsare da su a gidan wakafi. 

Kungiyar tawayen ta ELN ta ce Odin Sanchez na yanzu haka a hannun kwamitin kiyon lafiya na kungiyar, kuma nan gaba kadan za a dauke shi ta jirgi mai dirar ungulu zuwa birnin Choco na arewa maso gabashin kasar domin mika shi ga hannun hukumomi.