Kwalambiya ta nemi dauki kan 'yan hijira
May 11, 2018Talla
Shugaba Juan Manuel Santos ya yi kira ga al'ummomin kasa da kasa da su kai masu dauki. Ya fada wa kamfanin dillancin labaran Jamus na dpa cewa ba su saba da karbar 'yan gudun hijira da yawa haka ba. Ya ce suna tare da al'ummar Venezuela amma ban da gwamnati da ke jefa al'ummarta cikin hali na kaka na ka yi.
Rikici na siyasa da tattalin arziki shi ya sanya al'ummar ta Venezuela ke yin kaura zuwa Kwalambiya kamar yadda jami'an kula da shige da fice a Kwalambiya suka bayyana a Bogota inda suka ce fiye da 'yan Venezuela 650,000 ne ke rayuwa a Kwalambiya, kasar da ke da al'umma miliyan 49.