1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwalambiya: Ambaliya ta yi sanadin rayuka sama da 200

Yusuf Bala Nayaya
April 2, 2017

A cewar Kungiyar agaji ta RedCross akwai mutane 202 da suka samu raunika baya ga sama da 220 da suka bace sakamakon kwararar lakar.

https://p.dw.com/p/2aVu0
Kolumbien Mocoa,  Erdrutsch Evakuierung Mädchen
Hoto: picture-alliance/AA/Colombian Presidency

Torokon ruwan koguna uku da suka tumbatsa ya yi ambaliya da kwarar laka da ta mamaye wani karamin birni a Kwalambiya, lamarin da ya jawo halakar sama da mutane 200 da  rushe gidaje da awon gaba da motoci. Bala'in da ke zuwa lokacin da mutane ke barci a wannan gari.Wannan lamari dai ya faru ne bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya tun daga ranar Juma'a aka wayi gari Asabar ana maka shi, a yankin na Mocoa da ke da yawan tsaunika kusa da iyakar Equador da Kwalambiya.

Ruwan dauke da laka da ke tafe da sauri ya mamaye titinan birnin da jijjige bishiyu dauke da baraguzan duwatsu, ya afkawa wadannan al'umma da dama cikinsu ba tare da samun damar ficewa ba. A cewar Kungiyar agaji ta RedCross akwai mutane 202 da suka samu raunika baya ga sama da 220 da suka bace.

Tuni dai shugaba Juan Manuel Santos na Kwalambiya ya kafa dokar tabaci a wannan yanki inda ake tsammanin mutanen da suka rasu ta sanadin wannan bala'i zai iya karuwa.