1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwaco sansanin gwale-gwale na Auschwitz a ranar 27.01.1945

January 26, 2005

A ranar 27 ga watan janairu na 1945 ne sojojin Soviet suka kwaco sansanin gwale-gwale na Auschwitz inda aka kashe Yahudawa sama da miliyan daya

https://p.dw.com/p/BvdS
Hoton sansanin gwale-gwale na Auschwitz a misalin shekaru 60 da suka wuce
Hoton sansanin gwale-gwale na Auschwitz a misalin shekaru 60 da suka wuceHoto: dpa

A daidai ranar 13 ga watan janairun shekara ta 1945 ne askarawan Soviet suka gabatar da gagarumin matakinsu na kutse, inda aka shiga kazamar bata kashi a filin dagar dake da fadin murabba’in kilomita 1000. Sannu a hankali sojojin na Soviet suka rika kwato yankuna akan hanyarsu ta ‚yantar da fursinoni dubu takwas da suka rage a sansanin gwale-gwalen na Auschwitz. A kuma ranar asabar 25 ga watan janairun shekara ta 1945 sojojin suka isa Auschwitz a wajejen azahar. Amma fa dakarun sojan Jamus ‚yan gani kashenin akidar Hitler, sai suka ja daga domin a yi ta ta kare. Sai kuwa da aka halaka sojojin Siveit 231 a gumurzun da aka yi domin kwaco sansanin gwale-gwalen na Auschwitz. Fursinoni 650 suka yi asarar rayukansu, sannan ragowar da suka yi shaura kuma, kusan ba abin da ya banbantasu da gawawwaki. Ba a dai fito fili aka yi bayanin abubuwan da suka faru a Auschwitz ba, sai a wajejen tsakiyar watan afrilun shekarar ta 1945, wasu da suka kubuta daga wannan azaba suka rika gabatar da bayanai aka ta’asar da suka sha fama da ita a sashen harshen Jamusanci na tashar BBC. Daga cikinsu har da wata da ake kira Anita Lasker, inda ta ce an dirke wani kwamandan soja da wani likita a kofar sansanin gwale-gwalen, wadanda da zarar fursinonin sun fito suke tankade-da-rairaya, inda ake tambayar yawan shekarunsu da kuma matsayin lafiyarsu. Duk wani fursinan da yayi batan basira ya nuna wani ciwo da yake fama da shi, tamkar dai ya rattaba hannunsa ne akan wani hukunci na kisan da za a zartar masa. Yara da tsofaffi sune suka fi fama da radadin wannan ta’asa da kisan kai. Duk eanda aka yi hagu da shi to ke nan ya durfafi hanyar barzahu. Shi kuwa wanda ya tsira sai a tilasta masa aikin dole. Akwai wasu kamfanoni na Jamus kamarsu Krupp da suka ci gajiyar wannan aiki na bauta, wanda galibi fursinonin ba sa zarce tsawon watanni uku suna gudanar da shi ba tare da sun bakunci lahira ba. Kusan a kowane mako sai an yi tankade da rairaya a karkashin jagorancin wani likita mai suna Josef Mengele, wanda aka lakaba masa wai mala’ikan mutuwa. A kokarinsu na batar da gurabun ta’asar ta kisan kiyashi dakarun Hitler na SS suka tarwatsa dakunan da aka saba kashe fursinonin da hayakin gas suka kuma canza wa wasu daga cikinsu sansanoni a wajejen karshen shekarar 1944. A daidai lokacin da suka fara sauraron karatowar sojan Soviet, dakarun tsaro na Hitler SS da kuma sojojin Jamus suka tattara nasu ya nasu suka ranta a na kare suna masu tilasta wa duk wani fursina dake da koshin lafiya, lalle sai yayi musu rakiya a matsayin garkuwa, a yayinda suka baro wasu matattu kimanin dubu 65 a baya. A takaice an halaka mutane sama da miliyan daya a sansanin gwale-gwalen na Auschwitz, su kuma sojan Soviet suka tarar da fursinoni dubu bakwai da dari biyar a lokacin da suka isa sansanin a daidai ranar 27 ga watan janairun shekarar 1945.