Kuwaiti: Ana gudanar da zaben ′yan majalisa. | Labarai | DW | 26.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kuwaiti: Ana gudanar da zaben 'yan majalisa.

Al'ummar Kuwaiti na zaben 'yan majalisa, a wannan karamar kasa mai arzikin mai, wadda ke fama da matsalar tattali sakamakon faduwar darajar mai a kasuwannin duniya.

Zaben ya biyo bayan rusa majalisar dokokin kasar da Sarki ya yi a watan Oktoban da ya gabata, biyo bayan rage kudaden gudanar da karin farashin makamashin gas.

 

Kuwaiti ta kasance kasa daya tilo tsakanin takwarorinta masu arziki na yankin Gulf, da ke da tsarin siyasa mai sassauci, duk da cewar Basaraken kasar ne keda wuka da nama akan komai.

 

Majalisar mai wakilai 50 na da hurumin binciken ministoci, ciki har da wadanda suka fito daga gidan sarauta. Sai dai a baya-bayan nan afkawa 'yan adawa da kame kamesu, da sauya dokokin zabe, na dasa ayar tambaya dangane da ko sakamakon zaben na yau zai iya haifar da wani sauyi.