1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuri'a kan ficewar Birtaniyya daga EU na kawo mata cikas

Mohammad Nasiru AwalApril 27, 2016

Tattalin arzikin Birtaniyya ya fara yin rauni tun gabanin kuri'ar raba gardama kan ficewar kasar daga EU a ranar 23 ga watan Yuni.

https://p.dw.com/p/1IeJk
Großbritannien David Cameron im House of Commons
Firaminista David Cameron a gaban majalisar dokoki da ke birnin LondonHoto: picture-alliance/House of Commons

Tattalin arzikin Birtaniyya ya rasa tagomashi gabanin kuri'ar raba gardama game da cigaba da zaman kasar cikin Tarayyar Turai ko kuma ta fice. Ofishin kididdiga a birnin London ya ce daga watan Janeru zuwa Maris jimillar kayan da kasar ke samarwa a cikin gida ya tashi da 0.4 cikin 100 kacal. Tun farko masana tattalin arziki sun yi wannan hasashen bayan da a karshen shekarar 2015 bunkasar tattalin arzikin ba ta haura 0.6 cikin 100 ba. 'Yar kwarya-kwaryar bunkasar ta samu ne daga bankuna, yayin da fannonin gine-gine da masana'antu suka fuskanci koma baya. Kuri'ar raba gardama da za a gudanar a ranar 23 ga watan Yuni kan ficewar kasar daga kungiyar EU na sanya rashin tabbas ga tattalin arzikin kasar ta Birtaniyya.