1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuri´ar raba gardama akan daftarin tsarin mulkin Demukiradiyar Kongo

December 18, 2005
https://p.dw.com/p/BvFz

An bude rumfunan zabe a kasar JDK, inda jama´a ke zabe a kuri´ar raba gardama akan wani sabon daftarin kundin tsarin mulki wanda ke matsayin wani muhimmin mataki na kokarin da kasar ke yi na girke sahihiyar demukiradiya dake tafiyar hawainiya. An fara kada kuri´ar ne a gabashin kasar sannan awa daya baya aka bude rumfunan zabe a Kinshasa babban birnin kasar. Kimanin mutane miliyan 24.5 ne suka cancanci kada kuri´a a zaben wanda zai fid da kasar daga rikice-rikicen da ta yi fama da shi daga watan agustan shekarar 1998 zuwa watan desamban shekara ta 2002, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane kimanin miliyan 3.