1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kuriar raba gardama adangane da sakamakon bincike

Yan majalisaar dokokin turai na mahawara adangane da rahotan kammala binciken daya dauki shekara guda ana gudanarwa ,adangane zargin da akewa hukumar leken asirin Amurka ,na tsare wadanda ake zargi da aikata taadanci a wasu kasashen turai,tare da shigar da wasu wannan kasa da ake azabtar da mutane.A yau ne akesaran kada kuriar raba gardama dangane da sakamakon wannan bincike.Rahotan dai na zargin kasashen turai sama da 10 da suka hadar da Jamus da Britania da Poland da Spain,da laifin aikawa da mutanen da suke zargi da laifin taaddanci a asirce,sai dai babu tabbaci dangane da hakan.