1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuri'ar Raba Gardama a Game Da Sake Hadewar Tsuburin Cyprus

April 26, 2004

A kuri'ar raba gardama da aka gudanar a game da makomar sake hadewar tsuburin Cyprus ranar asabar da ta wuce, kimanin kashi 76% na Girkawan tsiburin suka bayyana adawarsu da shirin hadewar da MDD da gabatar, a yayinda kashi 65% na Turkawan tsuburin suka yi na'am da shi

https://p.dw.com/p/BvkI
Girkawa masu adawa da sake hadewar tsuburin Cyprus
Girkawa masu adawa da sake hadewar tsuburin CyprusHoto: AP

A hakika dai abin da ya wakana a tsibirin Cyprus ranar asabar da ta wuce, abu ne dake da ban mamaki. Domin kuwa an yi shekara da shekaru Turkawan tsuburin na adawa da duk wani matakin da za a dauka akan hanyar sake hadewar yankunan tsuburin guda biyu, yankin Turkawa da na Girkawa. Amma sai ga shi a kuri’ar raba gardamar da aka kada ranar asabar da ta wuce kimanin kashi 65% na Turkawan sun yi na’am da shawarar sake hadewar da MDD ta zayyana a yayinda su kuma Girkawan, kimanin kashi 76% daga cikinsu suka sa kafa suka yi fatali da wannan shawara. Bisa ga ra’ayin da yawa daga cikinsu shawarar ta MDD tana wa Turkawa alfarma fiye da kima. Amma a daya hannun ga alamu da yawa daga Girkawan Cyprus sun kasa ganewa ne cewar tsuburin ba na Girkawa ne su ya su ba, yanki ne da ya kunshi Turkawa tsiraru, wadanda ke da cikakken ikon fadin albarkacin bakinsu a harkokin tsuburin na yau da kullum. Rashin adalcin dake tattare da kuri’ar raba gardamar shi ne kasancewar duk da hana ruwa gudu da Girkawan suka yi, bangarensu zai samu cikakken ikon shigowa inuwar Kungiyar Tarayyar Turai tun daga ranar asabar daya ga watan mayu, a yayinda bangaren Turkawan zai ci gaba da zama saniyar ware, duk kuwa da biyayyan da Turkawan suka yi ga bukatar Kungiyar na yin na’am da shawarar sake hadewar ta MDD. Hukumar Kungiyar ta Tarayyar Turai, ba ta yi wata-wata ba wajen bayyana takaicinta game da sakamakon kuri’ar raba gardamar da kuma yin tofin Allah tsine akan abin da ta kira mataki na zalunci da tace labarai.

A hakika kuwa babu wani abin da za a yi rufa-rufa game da shi. Sakamakon kuri’ar raba gardamar a Cyprus ya sanya murna ta koma ciki dangane da manufofin ketare na Kungiyar Tarayyar Turai. Wannan tamkar sakayya ce ga sako-sako da kungiyar tayi wajen gindaya sharadin sake hadewar tsuburin kafin a karbi Cyprus a inuwarta. Wani abin takaici ma a nan shi ne yadda kungiyar ta ba da kai bori ya hau ga matakin ci da ceto da gwamnatin kasar Girka ta dauka na cewar ba zata amince da karbar illahirin kasashen gabacin Turai ba sai fa idan matakin ya hada da kudancin tsibirin Cyprus. A yanzu Kungiyar ta Tarayyar Turai zata wayi gari tare da wata kasa a karkashin tutarta, wacce ba a warware rikicin kabilanci da rarrabuwar da take fama da shi ba. Abu mafi alheri a halin yanzun dai shi ne a dubi matsalar Turkawan Cyprus da idanun basira saboda hali na sanin ya kamata da suka nunar. Wajibi ne a ba da la’akari da wannan batu lokacin da Kungiyar Tarayyar Turai zata yanke shawara a game da shiga shawarwarin karbar kasar Turkiyya a karshen wannan shekara. Ko da yake ba za a iya amincewa da bangaren Turkawan Cyprus a matsayin wata kasa mai cikakken ikon cin gashin kanta ba, amma wajibi ne a dauki matakai na gaggawa domin kakkabe yankin daga takunkumin karya tattalin arzikin da aka kakaba masa. Duk wani dari-dari da za ayi wajen daukar irin wannan mataki zai kai ga fid da kauna wajen sake hadewar tsuburin baki daya. A yanzun dai alhakin warware rikicin tsibirin na Cyprus ya rataya ne a wuyan Kungiyar Tarayyar Turai baki daya.