1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuri´ar amincewa da kundin tsarin mulkin kungiyar EU a majalisar dokoki ta Bundestag

Mohammad Nasiru AwalMay 12, 2005

Majalisar dokokin Jamus wato Bundestag ta kada kuri´ar amincewa da kundin tsarin mulkin kungiyar EU.

https://p.dw.com/p/Bvbz
Angela Merkel lokacin muhawwara akan kundin tsarin mulkin kungiyar EU a Bundestag
Angela Merkel lokacin muhawwara akan kundin tsarin mulkin kungiyar EU a BundestagHoto: AP

An dai yi ta tabi da sowa lokacin da aka ba da sakamakon kuri´ar amincewa da kundin tsarin mulkin KTT EU a majalisar dokoki ta Bundestag. Dukkan wakilan jam´iyun siyasa in ban da wakilai 23 daga bangaren jam´iyun adawa na CDU da CSU, sun kada kuri´ar amincewa da kundin tsarin mulkin na EU. Gabanin a kada kuri´ar sai da aka tabka muhawwara ta sama da sa´o´i 3. A farkon muhawwarar SGJ kuma dan jam´iyar SPD Gerhard Schröder ya bayyana tsarin mulkin na kungiyar EU da cewa abin tarihi ne.

„Kundin tsarin mulkin zai karfafa yanayin siyasa tare da inganta demukiradiyya da kusanta juna tsakanin al´umomin kasashen KTT. Hazalika tsarin mulkin zai bawa majalisar Turai karin ikon fada a ji a harkokin gudanarwa na kungiyar EU.“

A cikin jawabin na sa SG na Jamus ya fassara zamanin da aka kawo karshen yakin duniya na biyu kimanin shekaru 60 da suka wuce ya zuwa wannan lokaci da aka tsara kundin tsarin mulkin kungiyar EU da cewa wata kyakkyawar alama ce ta zaman lafiya da ta wanzu tsakanin abokan gaba juna a da wanda kuma har wayau ya kasance abin dogaro na tabbatar da makomar kungiyar EU. Shi kuwa a nasa bangare ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya jawo hankali ne da cewa yarjeniyoyin kungiyar EU na da ba zasu yi wani tasiri ba a cikin kungiyar mai wakilai kasashe 25 a cikinta.

„Duk mai kyaunar zaman lafiya a cikin Turai to dole ya yi na´am da shirin fadada Turai. Kuma duk wanda yayi haka to dole ne ya amince da wannan tsarin mulkli wanda ya tanadi fadada kungiyar EU a karkashin yarjeniyoyinta na da.“

Ita ma shugabar jam´iyar CDU Angela Merkel ta jaddada cewa tsarin mulkin zai karfafa mulkin demukiradiya a Turai, musamman dangane da sabon tsarin kada kuri´a cikin kungiyar, wanda ke ba da la´akari da yawan al´umar kasa. Angela Merkel ta ce hakan babbar nasara ce ga Jamus. Duk da haka shugabar ta jam´iyar CDU ta nuna rashin gamsuwa ga wasu sassa na tsarin mulkin, tana mai cewa:

„Mun yi fatan cewa da kamata yayi tsarin mulkin yayi bayani dalla-dalla game da tushenmu na addinan yahudu da nasara. Ko shakka babu in da an yi haka to da an bamu gagarumin taimako wajen danganta kanmu da addinan da muka yi imani da su.“

Kasancewar shugabannin jam´iyun CDU da CSU sun goyi da bayan tsarin mulkin, ya sa ba´a saurari masu sukar lamirin tsarin mulkin a cikin jam´iyun adawar ba.

Baya ga kundin tsarin mulkin na EU majalisar dokokin ta Bundestag ta kuma kada kuri´ar amincewa da sabuwar doka wadda zata ba ta karin ikon fada a ji cikin dokokin kungiyar EU. Yanzu haka dai a ranar 27 ga wannan wata na mayu majalisar dattawa ta Bundesrat zata kada ta ta kuri´ar, inda ake sa ran samun rinjaye kashi 2 cikin 3 da ake bukata.