kura ta lafa a Kismayo na kasar Somalia | Labarai | DW | 17.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

kura ta lafa a Kismayo na kasar Somalia

Kura ta lafa a fada tsakanin kungiyin yan tawaye 2 dake kokarin mallakar birnin Kismayo na kasar Somalia.

Majiyoyi daga asibiti dai sunce ya zuwa yanzu mutane 12 ne suka rasa rayukansu cikin fada na kawanaki uku tsakanin abokan gaban biyu.

Akalla mutane 33 suka samu rauni cikin tashe tashen hankula na baya bayan nan a kasar dake kahon Afrika inda ba doka da oda saboda rashin cikakkkiyar gwamnati tun 1991,wadda ta bada damar yake yake na kabilanci a kokarinsu na mallakar yankuna dabam dabam na kasar.

Jamian asibitin sunce mafi yawa na wadanda suka samu raunin suna jiyya a gidajensu saboda rashin magunguna da kayan aiki a asibitocin kasar.

Fada tsakanin kabilu dai ya zama ruwan dare a Somalia,tun lokacinda yan tawaye suka hambarar da gwamnatin tsohon shugaban mulkin danniya Muhammad Siad Barre shekaru 14 da suka shige.