Kura ta dan lafa a kone-konen mnotoci a kasar faransa | Labarai | DW | 10.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kura ta dan lafa a kone-konen mnotoci a kasar faransa

A Faransa an dan fara samun sa´ida, ga konen konen motocin da ke wakana, a yankunan ya ku bayi, daban daban na kasar.

A daren jiya motoci 394 kadai masu zanga zangar su ka kona.

Shekaran jiya 617, sannan daren litinin zuwa talata 1.173.

Daga farko wannan rikici, yau da sati 2 da su ka gabata, a jimilce, motoci dubu 6 da dari 4 ,su ka kone kurmus tare da gidaje da makarantu.

A daren jiya jami´an tsaro sun kama mutane 169.

A gaba daya a halin yanzu, mutane 2000, jami´an su ka kama a cikin wannan zanga zanga.

Bisa dukkan alamu, wannan sassauci, da a ka fara samu, ba zai rasa nasaba ba da dokar ta bace, da gwamnati ta kafa a yankunan da rikicin ya fi kamari, da kuma kiranye kiranye da jama´a ke ci gaba da yiwa masu zanga zangar.