Kungiyyar MEND tayi ikirarin hannu game da sabon hari a yankin | Labarai | DW | 08.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyyar MEND tayi ikirarin hannu game da sabon hari a yankin

Kungiyyar dake fafutikar kwatowa yankin Niger Delta yanci, wato MEND tace tana da hannu a cikin harin da aka kai kamfanin mai na

Agip dake BRASS a jihar Bayelsa a tarayyar Nigeria.

Harin na jiya alhamis, idan an iya tunawa ya haifar da yin garkuwa da wasu ma´aikatan man guda a kalla hudu,dukkansu yan kasar Italiya.

Ya zuwa yanzu dai kungiyyar ta MEND tayi kurarin ci gaba da kai irin wannan hari, har zuwa lokacin da gwamnatin tarayya zata biya musu bukatan su.

Daga cikin bukatun kungiyyar ta MEND, akwai batun sako shugabannin su guda biyu da ake ci gaba da tsare dasu.

Kurarin ci gaba da kai ire iren wadannan hare hare kuwa daga bangaren kungiyyar ta MEND, yazo ne kwanaki shida, izuwa taron kolin kasashe masu arzikin man fetur , da tarayyar Nigeria zata karbi bakoncin sa.