1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyyar Hamas ta kalubalanci Mr Abbas

Ibrahim SaniNovember 16, 2007
https://p.dw.com/p/CIBu

Magoya bayan ƙungiyyar Hamas sun gudanar da zanga zangar lumana, a kusa da gidan shugaba Mahmud Abbas dake Gaza. ´Yan ƙungiyyar na bukatar shugaban kare muradunsu ne, a lokacin taron kolin Yankin Gabas ta Tsakiya, da za a yi a birnin Annapolis dake Amirka.Batutuwan da ´ Yan ƙungiyyar ke son tabbatarwa Yankin na Palasɗinawa sun haɗar da birnin Jerusalem da kuma sako fursunonin siyasa da ake tsare dasu a Israela.

Kakakin ƙungiyyar, Mr Khalil al-Hayya, ya ce matukar Palasɗinawa ba su sami haka ba, to babu shakka akwai sauran tsalle a gaba.Ƙungiyyar dai ta Hamas a cewar rahotanni ba a gayyaceta taron sulhun yankin na Gabas ta Tsakiya ba. Amirka wacce ta ɗauki nauyin shirya taron, na tunanin gudanar da shi ne nan da wata ɗaya ko kuma biyu ma su zuwa.