1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

KUNGIYYAR EU TAYI NAMIJIN KOKARI

January 23, 2004
https://p.dw.com/p/BvmN
Da yawa daga cikin kungiyoyi masu zanan kansu a nahiyar Turai sun bayyana raayin su na maraba da yunkurin da kungiyyar tarayyar Turai wato Eu tayi na kara yawan kudin tallafi da tayi a cikin kasafin kundinta na shekara ta 2004 izuwa kasashen dake bukatar taimako na raya kasa. Kungiyoyin dai sun bayyana wannan raayin nasu ne dangane da irin matakan da kungiyyar ta Eu take dauka kann kara kula da kasashe maso tasowa na Africa dake fama da matsaloli iri daban daban na rayuwa.

To sai dai kuma a hannu daya kungiyoyin na cike da tunanin yadda makomar kasashen dake samun irin wannan tallafi zata koma a nan gaba sakamakon yunkurin da kungiyyar ta Eu keyi na kirkiro da ofishin ministan harkokin wajen kungiyyar da zai dinga kula da matakan da kungiyyar ke dauka kann kasashen waje wadanda ba mambobi bane a cikin kungiyyar ta Eu.

Bugu da kari kungiyoyin sun kuma yi fatan cewa sabuwar hukumar zartarwa ta kungiyyar da aka kirkiro zata sa ido wajen kula da ganin irin tallafin da kungiyyar ta Eu ke bayarwa na tafiya dai dai wa dai da ba tare da samun wani cikas ba.

A kuwa ta bakin shugaban daya daga cikin irin wadan nan kungiyoyi masu zaman kansu mai suna ECHO,cewa yayi yana sa ran tsoffin mambobin da kuma sabbi da zasu shiga watanni kadan masu zuwa zasu tsaya su natsu don karatun mun natsu wajen cimma yarjejeniya kann sabon kundin tsarin mulkin kungiyyar da aka dinga yin kace nane a kansa a watannin baya da suka shige.

Ta hanyar cimma irin wannan mataki ne a cewar MR Chaitkin kungiyyar zata samu hurumin ci gaba tare da karbuwa a tsakanin mambobinta,don samun saukin aiwatar da aiyukanta ba tare da wani tashin hankali ba.

A dai farkon shekarar nan ne kungiyyar ta Eu ta bayar da sanarwar karin yawan kudin tallafi da zata kashe ga kasashe dake da bukata,musanmamma na nahiyar africa don rasa kasashen nasu.

Yawan kudin tallafin dai a wannan shekara ya kai dala miliyan 611,a maimakon dala miliyan 551 data kashe a shekara ta 2003 data gabata. Wadan nan dai kudade kungiyyar ta Eu zata kashe sune ta hanyar kungiyoyi irin su Echo da hukumar bayar da agajin gaggawa ta mdd,irin su Red Cross da kuma wasu kungiyoyin da yawan su ya kai sama da dari biyu.

Bisa kuwa rahotanni da suka iso mana kungiyyar ta Eu zata kashe wadan nan kudadene na tallafi ne a kasashe kusan sama da hamsin. Kusan kuwa daya bisa ukun kasafin kudin tallafin na bana zai tafi ne izuwa kasashe da suka fito daga nahiyar Africa,kasashe irin su janhuriyar Dimokradiyyar Congo bisa kiyasi zata sami dala miliyan 50, sudan kuma dala miliyan 31 , Zimbabwe kuma dala miliyan23 da digo daya. Ragowar kasashen sun fito ne daga yankin gabas ta tsakiya irin su iraqi da sauran su. Bugu da kari akwai kuma kasashe irin su Iran Pakistan da Afganistan,wadanda dukkannin su zasu amfana da wannan tallafin na kungiyyar ta Eu.